Shekara 69: Shugaba Tinubu Ya Tuna Abotarsa da Kwankwaso, Ya Aika Masa da Sako
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa har yanzu tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso abokinsa ne
- Tinubu ya aika da sakon taya murna da fatan alheri ga Kwankwaso yayin da ya cika shekara 69 a ranar 21 ga watan Oktoba, 2025
- Shugaban ya tuna irin gudummuwar da Kwankwaso ya bayar tun lokacin da suke tare a Majalisa har kawo yanzu da ya koma NNPP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tuna abotarsa da jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Shugaba Tinubu ya taya Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda zai cika shekaru 69 a duniya gobe Talata.

Source: Facebook
Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar yau Litinin, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Bola Tinubu ya taya Kwankwaso murna
Bola Tinubu ya taya iyalan Kwankwaso, abokansa da ‘yan siyasa abokan hulɗarsa murna yayin da suke bikin wannan rana ta musamman.
Shugaban ƙasan ya yaba da irin gagarumar gudunmawar da Kwankwaso ya bayar wa ƙasar nan a matsayinsa na jagora a wurare daban-daban da ya taɓa riƙewa.
Ya tuna cewa Kwankwaso ya rike kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai a lokacin jamhuriya ta uku da ta rushe, sannan ya zama gwamnan Jihar Kano na tsawon wa’adin mulki biyu.
Haka zalika Kwankwaso ya taba zama Ministan Tsaro, da kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya in ji rahoton PM News.
Akwai abota tsakanin Tinubu da Kwankwaso?
Shugaban kasa ya jaddada cewa duk da Kwankwaso ya bar APC da suka kafa tare ya koma NNPP, har yanzu abotarsu ba ta rushe ba.
Tinubu ya ce irin tasirin Kwankwaso da shahararsa a Arewa, musamman a Kano, ya nuna yadda yake kaunar talakawa, kuma siyasarsa ta yi kama da ta marigayi Mallam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
Shugaba Bola Tinubu ya ce:
“Har yanzu Sanata Kwankwaso abokina ne, kuma abokin aiki, wanda muka yi aiki tare a majalisar dokoki a shekarar 1992, sannan muka sake haduwa a matsayin gwamnoni a 1999.
"Mun kuma yi aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC. Ko da yake daga baya ya bar jam’iyyar ya kafa NNPP, amma har yanzu yana cikin sahun masu akidar kawo ci gaba.”

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya yi masa fatan ƙarin lafiya, tsawon rai, da ci gaba da hidima mai tasiri ga ƙasar Najeriya.
Tinubu ya hadu da Kwankwaso a Ibadan
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaisa da Kwankwaso yayin da suka hadu a wurin nadin Olubadan na 44 a jihar Oyo.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin Kwankwaso ya shirya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
A wani faifan bidiyo da fadar shugaban kasa ta fitar, an ga Bola Tinubu ya gaisada Kwankwao cikin fara'aa wurin taron, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


