Jam'iyyar PDP da Sakatarenta na Kasa Sun Samu Sabani kan Takardar da Aka Aika Wa INEC
- Jam'iyyar PDP ta musanta zargin da sakatarenta na kasa, Samuel Anyanwu ya yi cewa an yi bogin sa hannunsa a wasu takardu
- Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba ya tabbatar da cewa Anyanwu da kansa ya sa hannu a takardun da jam'iyya ta tura wa INEC
- Wannan dai na zuwa ne bayan Sanata Anyanwu ya shigar da korafin jam'iyyarsa gaban DSS da Sufetan Yan Sanda na kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rikicin da ya kunno kai a babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya watau PDP kan batun sa hannun sakataren jam'iyya, Samuel Anyanwu ya dauki sabon salo.

Kara karanta wannan
Rigima ta kunno kai a jam'iyyar hadaka, an dakatar da mataimakin shugaban ADC na kasa
Tun farko dai Sanata Samuel Anyanwu ya yi zargin cewa sa hannunsa da aka gani a jikin takardar sanar da babban taron PDP na bogi ne.

Source: Twitter
PDP ta musanta ikirarin Sanata Anyanwu
Sai dai a yau Litinin, 20 ga watan Oktoba, 2025, kwamitin gudanarwa na PDP ta kasa (NWC) ya karyata ikirarin Anyawu, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.
Kwamitin NWC ya bayyana cewa zargin ƙirƙirar sa hannu na bogi da sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya yi ba gaskiya ba ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Ologunagba ya kuma tabbatar da cewa Anyanwu ne ya sa hannu da kansa a takardar da PDP ta aika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau (INEC).
Abin da ya kawo rikici kan sa hannun Anyanwu
Ya fadi haka ne a matsayin martani ga ikirarin da Anyanwu ya yi cewa an ƙirƙiri sa hannunsa a takardar da PDP ta aika wa INEC domin sanar da ita rana, lokaci da wurin da za a gudanar da babban taron PDP a Ibadan, Jihar Oyo.
Idan za ku iya tuna wa jam'iyyar PDP ta shirya gangamin taronta na kasa wanda za ta zabi shugabanni a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.
Sai dai takardar sanar da wannan taro a hukumance da PDP ta tura wa INEC dauke da sa hannun shugaban jam'iyya, Umar Damagum, da sakatare ta tayar da kura.
Sakataren PDP ya kai korafi DSS
Rahoton Leadership ya ce Anyanwu, wanda ake ganin yana goyon bayan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike a rigingimun da ke faruwa a PDP, ya yi ikirarin cewa bai sa hannu a takardar ba.
Bisa haka ne Anyanwu ya kai ƙara ga Hukumar Tsaro ta DSS da Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa (IGP), inda ya yi zargin cewa an kwafi sa hannunsa a wasu muhimman takardu na jam’iyyar.

Source: Facebook
Sai dai kakakin PDP na kasa, Ologunagba ya jaddada cewa Anyanwu da kansa ne ya sanya hannu a cikin takardun, yana mai cewa ba a kwafi sa hannunsa ba.
Ya kuma nuna wasu takardu da suka ƙunshi mu’amala tsakanin Anyanwu da sauran shugabannin PDP, da kuma tarukan kwamitin shirya taron da ya halarta, inda yake matsayin sakataren kwamitin.
PDP ta soki gwamnonin da suka koma APC
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce kwadayi da son kai ne ya sa wasu gwamnoninta suka sauya sheka zuwa APC.
Babbar jam'iyyar adawa ta sha alwashin cewa gwamnonin da suka bar ta za su girbi abin da suka shuka a zaben 2027.
PDP ta kuma bayyana cewa tafiyar gwamnonin ta kara zaburar da ita wajen tsaftace kanta da shirya wa babban zaben da ke tafe a Najeriya.
Asali: Legit.ng

