Yahaya Bello Ya Bukaci Tinubu Kada Ya Je Kamfen a Kogi, Ya Fadi Dalili

Yahaya Bello Ya Bukaci Tinubu Kada Ya Je Kamfen a Kogi, Ya Fadi Dalili

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta gudanar da babban taron siyasa a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, na daga cikin masu jawabi a wajen taron, inda ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Yahaya Bello ya nuna cewa shugaban kasan ba ya bukatar ya zo jihar Kogi domin yin kamfe a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya yi tsokaci kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Yahaya Bello ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya bukatar yin kamfen a jihar Kogi domin zaben shekarar 2027.

Yahaya Bello ya yabi Shugaba Bola Tinubu
Yahaya Bello tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce Yahaya Bello ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Kogi ranar Asabar, 18 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan bullo da wani shirin kifar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Yahaya Bello ya gayawa Tinubu?

Tsohon gwamnan ya ce jihar Kogi ta kasance gidan APC kuma jama’ar jihar suna da cikakken goyon baya ga shugaban kasa.

Hakazalika ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta da ’yan adawa a jihar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

“Mai girma shugaban kasa, ba ka bukatar zuwa jihar Kogi domin kamfen a 2027. Kada ka wahalar da kanka da kamfen a nan, saboda babu ’yan adawa a Kogi."
"Wadanda suke yin hayaniya a wasu wurare ba su taba ganin zakin Kogi ba. Muna taya ka murna, shugaban kasa. Kowace kasa mai girma tana bukatar shugaba da jama’a za su taru a kansa, kai ne wannan shugaba.”

- Yahaya Bello

Yahaya Bello ya yabawa Shugaba Tinubu

Yahaya Bello ya yabawa Shugaba Tinubu bisa irin jagorancinsa mai hangen nesa, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ta kawo ci gaba a bangaren tsaro, ayyukan more rayuwa, da karuwar kudaden shiga ga jihohi.

Kara karanta wannan

Wike na shirin yin takara da Tinubu a 2027? An ji gaskiyar zance

Yahaya Bello ya yabawa Shugaba Tinubu
Yahaya Bello tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook
"Muna godiya ga shugaban kasa bisa abubuwan da ya yi mana a Kogi da suka hada da nadin mukamai, ingantattun ayyuka, yaki da rashin tsaro, da karin kudin shiga ga jihohi."

- Yahaya Bello

Tsohon gwamnan, wanda ya jagoranci jihar daga 2016 zuwa 2024, ya kuma nemi goyon bayan sake zaben Shugaba Tinubu da Gwamna Usman Ododo a 2027.

A halin yanzu, manyan jiga-jigan jam’iyyar APC sun fara bayyana goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Tinubu kafin zaben shekarar 2027.

APC ta yi martanin shirin kifar da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta yi martani kan shawarar da Dele Momodu ya ba 'yan adawa ta yadda za su kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Mai magana da yawun jam'iyyar APC na jihar, Mista Seye Oloyede, ya bayyana cewa siyasar kabilanci ba za ta yi tasiri ba wajen hana sake zaben Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya yi kuskuren neman takara a 2027 ba'

Oloyede ya bayyana cewa a yanzu 'yan Najeriya sun samu wayewar da ba za su bari a yi kamfani da kabilanci ba wajen kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng