Wike Na Shirin Yin Takara da Tinubu a 2027? An Ji Gaskiyar Zance
- An yada wata jita-jita mai cewa ana shirin tursasa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi takara da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
- Sai dai, Ministan ya warware zare da abawa inda ya bayyana matsayarsa kan yin takarar shugaban kasa a shekarar 2027
- Nyesom Wike ya bayyana cewa har yanzu bai sauya ba daga kan goyon bayan da yake ga shugaban kasa Bola Tinubu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana shirin yin takara da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Wike ya karyata rahotanni da ke cewa ana shirin tsayar da shi takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Source: Twitter
Wike ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Lere Olayinka, wanda ya fitar da sanarwa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Wike ya yi shagube ga masu sauya sheka daga PDP zuwa APC duk da yana tare da Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Wike ya ce kan takara da Tinubu?
Ya bayyana cewa rahoton da wata kafar labarai ta yanar gizo ta wallafa, cewa wasu jagororin PDP na kokarin tursasa wa Wike shiga takarar shugaban kasa karya ce da wasu marasa aikin yi suka kirkira domin bata masa suna.
Wike ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu har zuwa shekarar 2031.
“Wike ba mutum ba ne da yake boye niyyarsa. Yana yin abin da yake faɗa, kuma yana faɗin abin da yake yi.”
- Lere Olayinka
Lere Olayinka ya ce Ministan ya bayyana a fili matsayinsa game da zaben shugaba kasan na shekarar 2027.
"Wike ya riga ya bayyana cewa a zaben shugaban kasa na 2027, yana tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
"A wurin Wike, shugaban kasa har zuwa 2031 shi ne Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana hakan a fili."
"Ba ya neman zama shugaban kasa, kuma ya mayar da hankali ne wajen tabbatar da nasarar manufar Renewed Hope Agenda ta shugaban kasa a birnin Abuja.”
- Lere Olayinka

Source: Twitter
Wike ya caccaki masu yada jita-jita
Lere Olayinka ya bayyana masu yaɗa jita-jitar a matsayin masu kokarin ɓata suna da hana ci gaba.
“Ministan ba ya yin aiki a boye. Yana faɗin abin da yake yi, kuma yana yin abin da yake faɗa,” in ji shi."
“Wike ya bayyana a fili cewa daga yanzu har zuwa 2031, zai tsaya ne bisa ga manufar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
- Lere Olayinka
Karanta wasu labaran kan Nyesom Wike
- Dangantaka ta yi tsami tsakanin Wike da Tinubu? An ji gaskiyar abin da ya faru
- Wike ya yaba da gwamnan PDP ya yanke shawarar sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Wike ya yi shagube ga masu sauya sheka daga PDP zuwa APC duk da yana tare da Tinubu
An bukaci Wike ya nemi afuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Rivers a karkashin jam'iyyar APC, Tonye Cole, ya bukaci Nyesom Wike, ya nemi afuwarsa.
Tonye Cole ya bukaci Naira biliyan 20 daga wajen ministan na babban birnin tarayya Abuja saboda zargin bata masa suna.
Tsohon dan takarar gwamnan ya dauki matakin ne bisa kalaman batanci da Wike ya yi gare shi wanda ya bata masa suna a bainar jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

