‘Dalilin da Ya Sa bai Kamata Jonathan Ya Yi Kuskuren Neman Takara a 2027 ba’

‘Dalilin da Ya Sa bai Kamata Jonathan Ya Yi Kuskuren Neman Takara a 2027 ba’

  • Tsohon dan majalisar tarayya kuma jigon jam’iyyar APC, Isra’el Sunny-Goli, ya gargadi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan sake takara
  • Isra’el ya bayyana cewa siyasar jihar Bayelsa ta canza kuma Jonathan mutum ne mai hangen nesa wanda ba zai bari a jefa shi cikin matsala ba
  • Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar PDP ta mutu a Najeriya, don haka babu wani abin da tsohon shugaban zai amfana idan ya sake fitowa takara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon dan majalisar tarayya a Najeriya ya yi maganganu kan yiwuwar sake tsayawa takara na Goodluck Jonathan a 2027.

Jigon APC, Isra'el Sunny-Goli ya bayyana cewa zai yi wahala tsohon shugaban kasa ya tsaya takara kamar yadda wasu yan siyasa ke yadawa.

Jigon APC ya ba Jonathan shawara kan sake tsayawa takara a 2027
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

Dan APC ya magantu kan takarar Jonathan

Kara karanta wannan

Ba tare da boye boye ba, PDP ta fadi dalilin da ya sa gwamnoninta komawa APC

Isra'el ya bayyana haka yayin wata hira da gidan talabijin na Channels wanda ta wallafa a YouTube a jiya Alhamis 16 ga watan Oktobar 2025.

Jigon APC ya bayyana cewa Jonathan ba zai yi kuskuren sake dawowa ba saboda zai ci karo da abin da bai yi tsammani ba.

Ya ce duba da yadda siyasar jihar Bayelsa ta sauya salo musamman yadda Gwamna Douye Diri ya yi murabus a PDP, komai na iya faruwa.

Ya ce:

"Ina tunanin Goodluck zai bi wannan lamari cikin fahimta saboda mutumin kirki ne kuma wanda yake son ci gaban jiharsa.
"Mutane suna son Jonathan ya sake dawowa domin yin takara a zabe amma na yi imanin cewa hakan ba daidai ba ne.
"Abubuwa a bayyane suke lamuran ba za su tafi masa daidai ba, mutane kawai suna zuwa wurinsa su ce ya fito takara saboda radin kansu."
An fadi dalilin da ya sa Jonathan bai zai yi takara ba
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yayin taro a ketare. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Getty Images

Abin da ka iya faruwa da Jonathan

Isra'el ya ce Jonathan mutum wayayye ne a siyasa wanda ya san daidai da akasin haka inda ya ce ba zai bari yan siyasar neman abinci su jefa shi a matsala ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Matsala ta tunkaro Gwamna Diri kan ficewa daga PDP

Ya tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ta mutu a Najeriya don haka babu abin da zai samu a cikinta idan ya ce zai yi takara a zaben.

"Amma Gooduck mutum ne wayayye da zai iya kauce fadawa tarkon yan siyasa masu neman na abinci, a wuri na bai kamata ya sake fitowa ba.
"Saboda sun sani cewa ba zai yi kuskuren sake neman takara ba saboda ko a Bayelsa ba zai samu goyon baya ba saboda kowa na son alaka da APC.
"Jam'iyyar PDP ta mutu a Najeriya, na yarda cewa Goodluck ba zai yi takara ba a zaben 2027 kamar yadda yan siyasa ke yadawa."

- Isra'el Sunny-Goli

Mutane na jan kunnen Jonathan kan takara

Kun ji cewa wasu yan siyasa da masu fashin baki sun yi ta gargadin tsohon shugaban kasa kan sake neman takara a zaben 2027.

Duk da Jonathan bai fito karara ya nuna aniyarsa ta sake neman mulkin Najeriya ba, amma wasu da ake ganin suna da kusanci da shi sun ce zai dawo siyasa a 2027.

Hakan na zuwa ne bayan ci gaba da kiran Jonathan ya sake fitowa domin neman takara a zaben 2027 da ake tunkara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.