Bayan Murabus din Gwamna Diri, Sanatan PDP Ya Koma Jam'iyyar APC

Bayan Murabus din Gwamna Diri, Sanatan PDP Ya Koma Jam'iyyar APC

  • PDP mai adawa a Najeriya ta sake samun koma baya a majalisar dattawa bayan ficewar daya daga cikin sanatocinta
  • Sanata Benson Konbowei mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai rinjaye
  • Ya bayyana cewa babu wani dan siyasan da ya san abin da yake yi da zai ci gaba da zama har sai PDP ta warware rikicinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata Benson Konbowei mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Benson Konbowei ya sanar da sauya shekarsa ne a zaman majalisar dattawa da aka gudanar a ranar Alhamis.

Sanata Benson Konbowei ya koma jam'iyyar APC
Sanata Benson Konbowei a zauren majalisar dattawa. Hoto: Dickson Didi Opuene
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce shugaban majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar da sanatan ya rubuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Sanata Benson ya fice daga PDP?

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Matsala ta tunkaro Gwamna Diri kan ficewa daga PDP

A cikin wasikar, ya bayyana dalilan da suka sa ya yanke shawarar barin PDP, jam’iyyar da ya kasance a cikinta tun shekarar 1998.

Sanata Konbowei ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da rashin jagoranci mai kyau da suka daɗe suna addabar jam’iyyar, wanda hakan ya hana ta zama ƙungiyar siyasa mai inganci.

“Dangane da yanayin rashin daɗi da rikicewar da PDP ke ciki, na yanke shawarar bin tafarkin gwamnan jihata, Sanata Douye Diri, wajen ficewa daga jam’iyyar.”

- Sanata Benson Konbowei

Sanatan ya bayyana cewa ya yi shawarwari da iyalansa, abokan siyasa, da manyan jiga-jigai na kasa kafin ya dauki matakin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.

Ya kara da cewa PDP ta rasa hanyarta ta asali da karfin da za ta iya lashe zaɓe har a matakin kananan hukumomi.

“Na rasa kwarin gwiwa a PDP. Ba ta da karfin taka rawar jam’iyyar da za ta iya lashe zaɓen kansila a kasar nan."

- Sanata Benson Konbowei

Sanata Konbowei ya tuna irin gudummawar da marigayi Alex Ekwueme da Solomon Lar, wadanda suka kafa PDP, suka bayar wajen gina jam’iyyar, yana mai cewa abin takaici ne yadda ta lalace a yanzu.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Fayose ya fadi gwamnonin da za su rage a jam'iyyar Jam'iyyar PDP

Sanata Benson ya koma APC

Ya ce yayin da zaɓen 2027 ke karatowa, babu ɗan siyasa mai hankali da zai ci gaba da jira PDP ta warware rikicinta mara iyaka.

“Saboda haka, na yanke shawarar yin murabus daga PDP tare da bayyana cikakkiyar biyayyata ga jam’iyyar APC."

- Sanata Benson Konbowei

Sanatan ya samo tarba daga wajen Akpabio

A cikin martaninsa, shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio, ya yi masa maraba zuwa cikin jam’iyyar APC yana mai cewa zuwansa zai karfafa aikin majalisar.

Sanata Benson Konbowei ya fice daga jam'iyyar PDP
Sanata Benson Konbowei tare da wasu sanatoci. Hoto: Bodmas Prince Kemepadei
Source: Facebook
“Muna maraba da Sanata Benson Konbowei cikin APC. Matakinka jarumta ce, kuma muna da tabbacin cewa gogewarka da jajircewarka za su taimaka wajen aikin da muke yi a majalisa."

- Sanata Godswill Akpabio

Gwamna Diri ya yi murabus daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Gwamna Diri ya yi murabus daga jam'iyyar PDP ne tare da 'yan majalisar dokokin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Bayan ficewar Peter Mbah zuwa APC, gwamnan PDP ya sake yin murabus

Hakazalika, ya bayyana cewa ya yanke shawarar tattara 'yan komatsansa daga PDP ne saboda wasu dalilai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng