Tsohon Gwamna Ya Ƙi Karbar Tayin Muƙami daga Shugaba Tinubu, Ya Faɗi Dalilansa
- Peter Obi ne kadai mai sauran karfi da tasiri a cikin ƴan adawa a Najeriya, cewar tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose
- Mista Ayodele Fayose ya jaddada cewa babu wanda zai iya doke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaben 2027
- Tsohon gwamnan ya kuma bayyana dalilin da ya sanya ya ƙi karɓar tayin muƙami da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa Peter Obi ne kadai ya rage mai sauran ƙarfi a cikin ƴan adawa a Najeriya.
Fayose ya ce duk da irin tasirin Obi a tsakanin matasa, babu wanda zai iya doke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaben 2027.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television ranar Laraba, inda ya yi tsokaci kan halin da adawa ke ciki da kuma makomar siyasar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Obi ne kadai muryar adawa a Najeriya”
A cewar tsohon gwamnan, jam’iyyun adawa sun raunana bayan zaben 2023, kuma babu wani jagoran adawa da ke da sauran tasiri kamar Obi.
Tsohon gwamnan na Ekiti ya bayyana cewa:
“Ku gaya min, wa zai iya doke APC? A kaf ƴan adawa, Peter Obi ne kawai ya rage mai ƙarfin faɗa a ji, amma sauran duk sun yi laushi."
Fayose ya kara da cewa ko da yake ba zai iya doke Tinubu ba, Obi yana da karfin magana da yanayin da ke jan hankalin jama’a, musamman matasa da ke neman canji.
Ya bayyana cewa sauran manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, sun rasa yardar jama’a, yana mai cewa, “Mutane ba sa sauraron su kamar da.”
“ADC ba za ta kai labari ba” - Fayose
Fayose ya kuma yi tsokaci kan hadin gwiwar ‘yan adawa da suka zabi ADC a matsayin jam'iyyar haɗakarsu gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: Fayose ya fadi gwamnonin da za su rage a jam'iyyar Jam'iyyar PDP
Ya ce jam’iyyar ADC ba za ta iya zama barazana ga APC ba saboda rashin karfi da hadin kai a tsakanin shugabannin da suka kafa ta.
“Su abokaina ne, tsofaffi da sababbi, amma gaskiya ita ce ADC ba ta da wata makoma, ba za su kai labari a 2027 ba,” in ji Fayose.
Tsohon gwamnan ya ce adawa tana bukatar sabon tsarin tunani da matasa masu hangen nesa idan har suna son kalubalantar gwamnati mai ci a gaba.

Source: Twitter
“Ban karbi mukami daga Tinubu ba”
Fayose ya bayyana cewa yana goyon bayan Shugaba Tinubu ne ba don neman riba ko mukami ba, amma don ganin Najeriya ta ci gaba.
A cewarsa, Tinubu ya taba tambayarsa me zai ba shi, sai ya amsa da cewa:
“Babu komai, mai girma shugaban kasa. Ni na gama ba da gudunmawa ta a hidimtawa jama'a, yanzu ina son na ƙarasa rayuwata cikin salama.”
Ya kara da cewa a shekarunsa 65, ba ya bukatar mukamin gwamnati, domin ya riga ya yi gwamna sau biyu kuma yana son ya mayar da hankali kan harkokin rayuwarsa.
"Tinubu zai samu tazarce" - Fayose
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ce, babu makawa Shugaba Bola Tinubu zai zarce a shekarar 2027.
Fayose, wanda jigo ne a PDP, ya ce haɗakar da wasu jagororin ‘yan adawa ke yi a ƙasar nan ba za ta iya hana Tinubu sake lashe zaɓe ba.
Ya ce ko da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari bai tsaya wa Tinubu a 2023 ba, amma duk da haka ya ci zaɓe, saboda ya fahimci lagon siyasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

