Sauya Sheka zuwa APC: Gwamnonin da Suka Rage a PDP bayan Ficewar Mbah da Diri

Sauya Sheka zuwa APC: Gwamnonin da Suka Rage a PDP bayan Ficewar Mbah da Diri

  • Jam'iyyar PDP mai adawa na ci gaba da rasa yawan gwamnonin da take da su a jihohin Najeriya
  • Wasu daga cikin gwamnonin da jam'iyyar take da su, sun tattara 'yan komatsansu zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Hakan ya sanya adadin gwamnonin da jam'iyyar PDP ke tunkahon tana da su ya ragu zuwa guda takwas kacal

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP ta samu a nakasu a yawan gwamnonin da take da su.

PDP yanzu ta koma mai gwamnoni takwas kacal bayan da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, da takwaransa na Bayelsa, Douye Diri, suka raba gari da jam'iyyar.

Yawan gwamnonin PDP ya ragu a Najeriya
Gwamna Bala Mohammed tare da wasu jagororin PDP. Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP a ranar Laraba, 15 ga watan Oktoban 2025.

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun ragu

Kara karanta wannan

PDP ta aika sako ga Tinubu bayan Gwamna Mbah ya sauya sheka zuwa APC

Wannan sabon sauyin na siyasa ya kara raunana karfin PDP, wadda ta taba rike jihohi 11 bayan babban zaben 2023.

Da wannan ci gaban, APC yanzu tana mulkin jihohi 24, yayin da PDP ke da jihohi takwas, sannan jam'iyyun LP, APGA, da NNPP ke da jiha daya kowacce.

Gwamna Peter Mbah ya sanar da sauya shekarsa zuwa APC a ranar Talata, kuma jam’iyyar ta karbe shi hannu bibbiyu.

Bayan kwana daya kacal, Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya tabbatar da ficewarsa daga PDP a wani taron manema labarai a Yenagoa, yana mai cewa hakan ya faru ne saboda wasu dalilai.

Gwamnonin da suka rage a PDP

Jaridar The Punch ta ce a halin yanzu, gwamnonin PDP da suka rage a jam'iyyar sune:

  1. Adamawa – Ahmadu Fintiri (Arewa maso Gabas)
  2. Bauchi – Bala Mohammed (Arewa maso Gabas)
  3. Plateau – Caleb Mutfwang (Arewa ta Tsakiya)
  4. Taraba – Agbu Kefas (Arewa ta Tsakiya)
  5. Zamfara – Dauda Lawal (Arewa maso Yamma)
  6. Oyo – Seyi Makinde (Kudu maso Yamma)
  7. Rivers – Siminalayi Fubara (Kudu maso Kudu)
  8. Osun – Ademola Adeleke (Kudu maso Yamma)

Kara karanta wannan

Bayan ficewar Peter Mbah zuwa APC, gwamnan PDP ya sake yin murabus

Sai dai ana ta rade-radin cewa wasu daga cikin wadannan gwamnoni, musamman na Taraba, Agbu Kefas, na iya sauya sheka nan gaba, kodayake babu wanda aka tabbatar da sauya shekarsa a hukumance.

Gwamnonin PDP sun rage yawa a Najeriya
Wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Twitter

Gwamna Bala ya koka kan ficewa daga PDP

Wannan sabuwar guguwar sauya sheka ta biyo bayan fargabar da shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana kwanan nan.

Gwamna Bala ya nuna damuwa kan yadda gwamnoni da manyan jiga-jigai ke barin jam’iyyar PDP suna komawa APC.

Da yake jawabi a Abuja ranar Asabar bayan ya kaddamar da kwamitin sadarwa na babban taron PDP, Bala Mohammed ya amince cewa sauya shekar ya girgiza jam’iyyar.

Sai dai, ya ce ana kokarin hada kan ‘ya’yan jam’iyyar gabanin babban taron na kasa da za a yi a birnin Ibadan daga 15 zuwa 16 ga Nuwamba 2025.

PDP ta gargadi Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta aika da sakon jan kunne ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyyar PDP ta gargadi Shugaba Tinubu kan ya daina sayen masu sauya sheka zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tauraruwar Kano ta kara haskawa, jihar ta samu babban nasara a sauyin yanayi

Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya bada tabbacin cewa ko kadan hakan ba zai taimaki Shugaba Tinubu ba a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng