PDP Ta Aika Sako ga Tinubu bayan Gwamna Mbah Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta ja kunnen Bola Ahmed Tinubu kan sauya shekar da wasu 'yan siyasa ke yi zuwa APC
- Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba ya bayyana cewa sauya sheka ba za ta taimaki Shugaba Tinubu ba
- Kakakin PDP ya bukaci ya maida hankali wajen cika alkawarin da ya daukarwa 'yan Najeriya kafin hawa kan ragamar mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya aika da sakon gargadi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Debo Ologunagba ya bukaci Tinubu ya daina abin da ya kira “sayen masu sauya sheka", yana mai cewa irin wannan dabara ta siyasa ba za ta sanya jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben 2027 ba.

Source: Twitter
Mai magana da yawun na PDP ya bayyana hakan ne a shirin 'Morning Brief' na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 15 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Debo Ologunagba ya yi gargadin ne yayin da yake mayar da martani kan sauya shekar gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, daga PDP zuwa APC.
Wane sako PDP ta ba Tinubu?
Ya ce jam’iyyar da ke mulki ta mayar da hankali wajen jan hankalin ‘yan adawa zuwa gare ta, maimakon magance matsalolin tattalin arziki da shugabanci da suke addabar kasar nan.
“Na taba fada wa shugaban kasa cewa ya daina wannan abin da yake yi na neman masu goya masa baya ko sayen masu sauya sheka, saboda hakan ba zai taimaka masa a 2027 ba."
“Zaben 2027 ba tsakanin PDP da APC bane, tsakanin APC da al’ummar Najeriya ne.”
- Debo Ologunagba
PDP ta yi zargi kan gwamnatin Tinubu
Debo Ologunagba ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu tana amfani da batun sauya sheka don karkatar da hankalin jama’a daga gazawarta.
“Abin da ke faruwa yanzu yana kawar da hankalinmu daga ainihin matsalar gwamnati. Ana yin haka ne domin a dauke hankali daga gazawarsu. Duk lokacin da muke tattauna PDP ko LP, muna mantawa da gazawar gwamnati."
- Debo Ologunagba
Ya jaddada cewa dimokuradiyya a Najeriya tana bukatar ra’ayoyi daban-daban da ‘yancin bayyana su, yana mai shawartar Shugaba Tinubu da ya rungumi hakuri, fahimta da hada kan kowa a cikin mulkinsa.

Source: Facebook
"Dole shugaban kasa ya fahimci cewa akwai nauyi a kansa wajen tabbatar da cewa kasar da ke da kabilu da ra’ayoyi daban-daban kamar Najeriya ta samu damar da kowa zai iya bayyana kansa."
“Ba lallai kowa ya yarda da kai ba, amma dole ne ka saurari mutane ka bar su suyi tasiri ta hanyarsu, domin hakan ne zai gina dimokuradiyya mai karfi da kasa mai cikakken ci gaba.”
- Debo Ologunagba
Gwamna Diri ya yi murabus daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa.
Gwamna Douye Diri ya sanar da yin murabua daga PDP ba tare da sanar da jam'iyyar da zai koma ba.
Hakazalika, Kakakin majalisar jihar Bayelsa, Abraham Ngobere da ‘yan majalisa 18 na PDP sun yi murabus tare da Gwamna Douye Diri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


