2027: Majalisa Ta Yi wa 'Yan Najeriya Albishir kan Gyaran Dokar Zabe
- Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa ana aiki tukuru domin a kammala gyaran dokar zaɓe kafin babban zaben 2027 mai zuwa
- Sanata Opeyemi Bamidele da ya bayyana haka ya ce matakin zai tabbatar da amfani da sabuwar doka a zaɓen da za a gudanar
- Gyaran dokar na cikin shirye-shiryen da ake yi na sake duba kundin tsarin mulki na 1999 da yi wa dokar zabe ta 2022 kwaskwarima
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana aiki a kan dokar INEC.
Sanata Bamidele ya ce ana aikin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022 a yanzu haka, kuma zai kammala kafin ƙarshen watan Disamba 2025.

Kara karanta wannan
Daga karshe, an garzaya da ministan Tinubu ketare domin jinyar cutar da ke damunsa

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Bamidele, wanda ke wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, ya bayyana hakan ne a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar Tarayya na aiki a kan dokar zabe
The Nation ta ruwaito cewa Bamidele ya bada tabbacin bayan shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanto wasikar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wasikar da Shugaban Kasa ya aika wa Majalisa na neman amincewar Sanatoci kan naɗin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan.
Tinubu ya naɗa Farfesa Amupitan, wanda masani ne a fannin shari’a, bayan amincewar Majalisar Koli ta Ƙasa bayan karewar wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu.
Majalisa na son a samu ingantaccen zaɓe
Sanata Bamidele ya bayyana cewa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta kasa rattaba hannu a gyaran karshe na dokar zaɓe a 2022.
Ya bayyana cewa dalilin hakan kuwa shi ne saboda makarar da aka yi wajen tura dokar daga majalisar zuwa fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Dalilin majalisa na kafa kwamiti kan zargin yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya
A kalaman Sanata Bamidele:
“Lokacin da aka gano wasu kura-kurai da suka hana wasu wakilai halartar taro, majalisa ta nemi gyara, amma tsohon shugaban ƙasa Buhari ya ce lokaci ya kusa da zaɓe sosai, kuma bai so jama’a su yi fassara ta daban."

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa:
“A wannan karo, kafin Disamba 2025, za mu tabbatar mun kammala gyaran domin sabuwar dokar ta fara aiki kafin zaɓen 2027.”
Bamidele, wanda kuma mataimakin shugaban kwamitin sake duba kundin tsarin mulki ne, ya ce an haɗa hannu da muhimman masu ruwa da tsaki.
Ya ce majalisa ta 10 tana da ayyuka masu yawa a wannan zama, ciki har da gyaran dokar zaɓe ta 2022 da kuma sake duba kundin tsarin mulki na 1999
'Yan Majalisa na son a dawo da zabe 2026
A baya, kun ji cewa Majalisar dokokin Najeriya na kan shirin sauya lokacin babban zaɓe daga Fabrairu 2027 zuwa Nuwamba 2026 a wani ɓangare na kudirin gyaran dokar zaɓe.
An bayyana wannan mataki ne a wani taron jin ra’ayin jama’a da majalisar ta shirya, inda aka tattauna sassa daban-daban na kudirin domin kara inganta harkokin zaɓen Najeriya.
Shugaban kwamitin harkokin zaɓe na majalisar, Hon. Adebayo Balogun, ya ce manufar sauyin ita ce tabbatar da cewa an kawar da ƙorafin zaɓe kafin shugabanni su hau mulki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
