Sauya Shekar Gwamnan Enugu: Cikakken Jerin Jihohi 24 da Yanzu Ke karkashin APC

Sauya Shekar Gwamnan Enugu: Cikakken Jerin Jihohi 24 da Yanzu Ke karkashin APC

  • Gwamna Peter Ndubuisi Mbah ya kara karfin jam'iyyar APC mai mulki, bayan sauya shekar da ya yi daga PDP a makon nan
  • A ranar Talata ne gwamnan jihar na Enugu ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC a hukumance gabanin zaben 2027
  • A cikin wannan rahoto, Legit Hausa ta tattaro jihohi 24 da yanzu suke karkashin APC bayan sauya shekar Douye Diri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A wani sabon sauyin siyasa da aka samu, gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a kasa.

A wani jawabin kai tsaye da ya yi a ranar Talata, Gwmana Mbah ya sanar da kawo karshen mulkin PDP na tsawon kusan shekaru 30 a Enugu.

Sauya shekar Gwamna Peter Mbah ya sa jam'iyyar APC na mulki a jihohi 24
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah tare da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: @PNMbah
Source: Facebook

Sauya shekar gwamnan Enugu zuwa APC

Kara karanta wannan

PDP ta aika sako ga Tinubu bayan Gwamna Mbah ya sauya sheka zuwa APC

A cikin jawabin nasa, Gwamna Mbah ya ce ya sauya shekar ne domin samun damar jagorantar Enugu zuwa tudun mun tsira ta hanyar hada kai da tarayya, cewar rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, da taimakon gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, jihar Enugu za ta samu ci gaba mai yawan gaske.

Wannan sauya shekar ta Mbah ta zo ne bayan an samu makamantanta a 2025, ciki har da sauya shekar Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da takwaransa na Akwa Ibom, Umo Eno, wadanda suka koma APC.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba, Gwamnan Bayelsa Douye Diri da na Tabara, Agbu Kefas za su sauya sheka zuwa APC.

Abin da sa Mbah ya bar jam'iyyar PDP

Gwamnan Mbah wanda aka zaba a karkashin PDP a 2023, ya kare sauya shekar da ya yi zuwa APC, yana mai cewa, mataki ne da ya zama dole don ci gaban Enugu.

"PDP ta rasa kunnen sauraron bukatun jama'a," a cewar Gwamna Mbah, lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Gwamnan jihar na Enugu ya kuma yi kalaman yabo ga Tinubu, wanda ya kira shi da "abokin fitar kunya," inda ya ce hadakar tarayya da Enufu za ta bunkasa tattalin arzikin jama'arsa.

Kara karanta wannan

Bayan ficewar Peter Mbah zuwa APC, gwamnan PDP ya sake yin murabus

Jam'iyyar APC ta mamaye jihohin Najeriya

Kafin sauya shekar Gwamna Mbah, jam'iyyar APC na da iko ne a jihohi 23, har zuwa watan Yunin 2025. Amma yanzu da Enugu ta shiga cikinta, jam'iyyar ta koma iko a jihohi 24, lamarin da ya bar PDP da jihohi takwas kacal (daga 10.)

Sauran jihohin kasar sun rarrabu ne tsakanin jam'iyyun siyasa marasa rinjaye: LP (1), APGA (1), da NNPP (1).

Jihohi 24 da APC ke mulki a Najeriya

  1. Akwa Ibom
  2. Benue
  3. Borno
  4. Cross River
  5. Delta
  6. Ebonyi
  7. Edo
  8. Ekiti
  9. Enugu
  10. Gombe
  11. Imo
  12. Jigawa
  13. Kaduna
  14. Katsina
  15. Kebbi
  16. Kogi
  17. Kwara
  18. Lagos
  19. Nasarawa
  20. Niger
  21. Ogun
  22. Ondo
  23. Sokoto
  24. Yobe

Jihohi 8 da ke karkashin PDP

  1. Adamawa
  2. Bauchi
  3. Osun
  4. Oyo
  5. Plateau
  6. Rivers
  7. Taraba
  8. Zamfara
  • Bayelsa (Gwamna Douye Diri ya sanar da barin PDP a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025)

Jam'iyyar LP

  • Abia

Jam'iyyar APGA

  • Anambra

Jam'iyyar NNPP

  • Kano
Jam'iyyar APC dai na ci gaba da samun karfi a Najeriya, inda yanzu take da jihohi 24 a karkashinta.
Hoton tutar jam'iyyar APC. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: UGC

Dalilan da ke jawo sauyin sheka

Masana sun ce dalilai da dama ne suka haifar da wannan sauyi. Na farko shi ne ƙoƙarin gwamnoni na kusantar gwamnatin tarayya domin samo abubuwan ci gaba ga jiharsu,

Kara karanta wannan

Bayan sauya sheka zuwa APC, Gwamna Mbah ya bijiro da bukatar sakin shugaban IPOB

Na biyu, PDP na fama da rikice-rikicen cikin gida da rashin daidaito tsakanin jagororinta, wanda ya tilasta wasu barin jam'iyyar.

A wani rahoton Legit Hausa, jagoran APGA, Chekwas Okorie ya ce yawancin gwamnoni na tserewa zuwa APC saboda tsoron EFCC bayan karewar wa’adinsu a mulki.

Ya zargi majalisar tarayya da zama 'yar amshin shata, musamman wajen gaza hana sauya sheka ba bisa ka’ida ba tsakanin jam’iyyu

Ana ganin cewa jam’iyyar na bukatar ta sake fasalinta, la'akari da yadda take ci gaba da rasa manyan mambobi saboda rashin daidaito da rashin sababbin dabarun siyasa.

A cewar wani rahoto daga jaridar The Nation, wasu gwamnoni biyu na PDP ma suna shirin bin sawun Mbah kafin ƙarshen shekarar nan, lamarin da zai kara raunana jam’iyyar.

Gwamnan Bayelsa ya fice daga PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwana daya bayan sauya shekar gwamnan PDP, takwaransa daga jam'iyyar ya yi murabus daga cikinta.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sanar da barinsa jam’iyyar PDP a wani taro da aka gudanar a gidan gwamnati ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An ji dalilin da ya sa gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Kakakin majalisar jihar, Rt Hon. Abraham Ngobere, da wasu ‘yan majalisa 18 na PDP suma sun bi sawunsa wajen yin murabus daga jam’iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com