Bakary: Dan Adawar Kamaru Ya Ce Ya Kayar da Paul Biya a Zaben Shugaban Kasa
- 'Dan adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Lahadi
- Gwamnatin Kamaru ta gargadi jama’a cewa hukumar tsarin mulki ce kaɗai ke da hurumin ayyana sakamakon zaben da aka yi
- Wasu na ganin Paul Biya, wanda ke da shekara 92 a duniya kuma yana mulki tun sama da shekara 40 ne ke kan gaba wajen sake lashe zabe
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kamaru - Zaɓe a ƙasar Kamaru ya ɗauki sabon salo yayin da ɗan adawa, Issa Tchiroma Bakary, ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa.
Rahotanni sun nuna cewa sanarwar ta zo ne kafin hukumomin ƙasa su fitar da cikakken sakamako na hukuma.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta ce Tchiroma ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta da safiyar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bayanin da ya yi, ya nemi shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, wanda ke da shekaru 92, da ya kira shi ya taya shi murna bisa abin da ya kira “zabin jama’a.”
Sai dai gwamnatin ƙasar ta Kamaru ta yi gargadi da cewa hukumar tsarin mulki ita ce kaɗai ke da ikon bayyana wanda ya lashe zaɓen.
Sanarwar Tchiroma ta jawo ce-ce-ku-ce
A cikin bidiyon da aka ɗauka a garinsa na Garoua, Tchiroma ya yi ikirarin lashe zaben shugaban kasa yana mai cewa:
“Jama’a sun zaɓa, kuma dole ne a mutunta wannan zaɓi.”
Ya ƙara da cewa, abin da ya fi dacewa shi ne shugaban ƙasa Paul Biya ya amince da sakamakon da kuma miƙa mulki cikin ruwan sanyi.
Tchiroma wanda tsohon kakakin gwamnati ne, ya yi aiki tare da Biya na tsawon shekaru 20 kafin ya yi murabus.

Source: Getty Images
Daga baya, ya shiga fafutukar neman mulki tare da samun goyon baya daga wasu jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula.
Matsayar gwamnatin Kamaru kan sanarwar
Duk da ayyana nasara da dan adawa Tchiroma ya yi, gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye ba.
Sai dai Ministan Harkokin Cikin Gida, Paul Atanga Nji, ya tunatar da cewa duk wanda ya bayyana sakamakon zabe ba tare da izini ba ya aikata babban laifi.
Ya ce a dokar zaɓe ta Kamaru, sakamako na wucin gadi na iya bayyana a rumfunan zaɓe, amma dole ne hukumar tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon kafin a ayyana wanda ya lashe.
Kiraye-kirayen girmama zabe a Kamaru
Tchiroma ya bayyana cewa nasararsa “sabon babi ne a tarihin Kamaru,” yana mai cewa jama’a sun nuna rashin amincewa da gwamnatin Biya bayan shekaru 43 na mulki.
Ya nemi sojoji da hukumomi su “tsaya tare da jama’a,” ba wai su zama 'yan amshin shata ga wasu ba.
BBC ta rahoto ya ce:
“Shugaba Paul Biya zai nuna dattaku da kwarewar siyasa idan ya girmama abin da suka zaba.”
Ya kuma gode wa sauran ‘yan takara da suka taya shi murna, yana mai cewa hakan alama ce ta wayewar kai da karfin dimokuradiyyar Kamaru.
Ana son sauya lokacin zaben Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin Najeriya na son sauya lokacin gudanar da babban zaben 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan na cikin shirye shiryen majalisar na gyara a tsarin zaben Najeriya.
Baya ga sauya lokacin zabe, majalisar na da niyyar kawo dokar da za ta ba jami'an tsaro, jami'an INEC da sauransu damar kada kuri'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


