Abin Boye Ya Fito: An Ji Dalilin da Ya Sa Gwamnan PDP Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Gwamna Peter Mbah ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yana mai cewa tsohuwar jam’iyyarsa ta kasa biyan bukatun mutanensa
- Mbah ya ce matakin da ya dauka ya samu goyon bayan tsohon gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, 'yan majalisar jiha da na tarayya
- Gwamnan ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga APC ne domin tabbatuwar muradun 'yan Enugu da samar masu da ci gaba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu – Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya tabbatar da ficewarsa daga PDP tare da shiga jam’iyya mai mulki a kasa, watau APC.
A yayin sauya shekar, Gwamna Mbah ya yi maganganu, amma abin da ya fi jan hankali shi ne, cewa "PDP ta rasa alkibla da tsarin da ya sa mutane suka shige ta."

Source: Twitter
Gwamnan Enugu ya bar PDP zuwa APC
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa wani rahoto a shafinsa na X, game da dalilin Peter Mbah na shiga jam'iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin rahoton, Onanuga ya ce gwamnan na Enugu ya gabatar da jawabi ga al’ummar Enugu a safiyar Talata, inda ya ce lokaci ya yi da zai dauki “matsaya mai karfi domin tabbatar da muradun jama’a”.
An jiyo Gwamna Peter Mbah yana cewa:
“Mun yanke shawarar barin jam’iyyar PDP domin shiga APC. Bayan shekaru kusan 30 muna tare da PDP, lokaci ya yi da za mu dauki sabuwar hanya domin makomar mu,” in ji Mbah.
Tsohon gwamna, 'yan majalisu sun koma APC
Peter Mbah ya tabbatar da cewa wannan sauya shekar ba ta sa ba ce shi kadai, domin ya bar PDP tare da shiga APC tare da tsohon gwamna, Ifeanyi Ugwuanyi.
Hakazalika, ya ce a tare da shi, akwai kwamishinoni, mambobin majalisar jiha da ta tarayya, da shugabannin jam’iyya fiye da suka sauya shekar tare, kamar yadda muka ruwaito.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar, Sullivan Chime yana daga cikin jagororin APC da suka halarci taron sauya shekar.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
“Mun gode wa PDP saboda irin goyon bayan da ta ba mu a baya, amma lokaci ya yi da za mu tsaya wajen tabbatar da abin da ke amfanar da jama’a."
- Gwamna Peter Mbah.

Source: Twitter
Dalilan Gwamna Mbah na komawa APC
Gwamnan ya ce sauya shekar tasa ta samo asali ne daga bukatar ganin al'ummarsa sun cika muradunsu, kuma sun samu wakilci da mutuntawa a matakin kasa.
Ya kuma bayyana cewa yana ganin hadin kai tsakaninsa da shugaban kasa Bola Tinubu zai haifar da sauyi mai amfani ga yankin Kudu maso Gabas.
"A yau, mun yanke shawarar barin PDP, kuma mun amince gaba daya cewa za mu shiga jam'iyyar APC.
"Akalla shekaru 30 PDP ke jagoranci a jihar Enugu, kuma an samu ci gaba a tsawon wannan lokaci na hadin kai.
"Sai dai, shi shugaba yakan yanke wasu matakai da za su iya zama masu tsauri a yayin da yake kokarin kawo ci gaba ga jama'arsa.
"Kuma akwai lokacin da dole ne kowanne daga cikinmu ya dauki matakai masu tsari da za su iya sauya kaddarar rayuwarsa."
“Ina ganin hadin kai da shugaban kasa Bola Tinubu zai kawo sauyi mai ma’ana ga jama'armu. Muna da hango ma kanmu ci gaba, kuma dole sauyi ya zama mai tsauri."
- Gwamna Peter Mbah.
Mukarraban Gwamna Mbah sun bar PDP
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan majalisar zartarwar jihar Enugu sun bar PDP, inda APC ta karbe su a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025.
Hadiman Gwamna Peter Mbah, ciki har da kwamishinoni, sun bayyana goyon bayansu ga APC, inda suka rera yabo ga Shugaba Bola Tinubu.
Masana na ganin cewa wannan sauyin siyasa zai sanya Enugu ta zama jiha ta farko daga Kudu maso Gabas da ke karkashin APC tun bayan 2023.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

