'Da Sake,' 'Yan Adawa Sun Yi Martani kan Dawo da Zaben 2027 zuwa 2026

'Da Sake,' 'Yan Adawa Sun Yi Martani kan Dawo da Zaben 2027 zuwa 2026

  • Majalisar dokokin tarayya na shirin dage babban zaben 2027 zuwa watan Nuwamba 2026 domin a samu isasshen lokaci kafin rantsar da shugabanni
  • Wasu jam’iyyun adawa na ganin wannan mataki dabara ce ta tsawaita wa’adin Shugaba Bola Tinubu, yayin da wasu ke cewa zai inganta tsarin zabe
  • Shirin sauya lokacin zaben na cikin kudirin sauya dokar zabe ta 2022 domin tabbatar da kammala kararrakin zabe kafin ranar 29 ga Mayun 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Shirin majalisar dokokin na neman matsar da babban zabe da na gwamnoni daga watan Fabrairu ko Maris zuwa watan Nuwamba 2026 ya haifar da sabani a tsakanin jam’iyyun adawa.

Wasu daga cikinsu na ganin hakan dabara ce da za ta bai wa gwamnatin Tinubu karin lokaci kafin sauya mulki, yayin da wasu ke cewa matakin zai taimaka wajen gyara tsarin gudanar da zabe.

Kara karanta wannan

Gwamnan Taraba ya dauki mataki na sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

Katin zaben Najeriya
Katin zabe da ake kada kuri'a da shi a Najeriya. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta ce shirin na daga cikin sauye-sauyen da ake son yi wa dokar zabe ta 2022 domin kammala dukkan shari’o’in zabe kafin ranar 29, Mayun 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me sabuwar dokar zabe ta tanada?

A cikin sabon kudirin, an bayyana cewa za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na gwamnoni a kalla kwanaki 185 kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci.

Vanguard ta wallafa cewa hakan na nufin cewa babban zaben gaba zai fado a watan Nuwamban 2026, kusan wata shida kafin wa’adin gwamnati mai ci ya kare.

Shugaban kwamitin majalisa kan harkokin zabe, Adebayo Balogun, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce tabbatar da cewa an kammala kararrakin zabe tun kafin rantsar da shugabanni.

Haka kuma an gabatar da shawarar rage lokacin shari’ar zabe daga kwanaki 180 zuwa 90 a kotun farko, sannan daga 90 zuwa 60 a kotun daukaka kara.

Ra’ayoyin jam'iyyun PDP da NNPP

Mataimakin shugaban matasa na jam’iyyar PDP a kasa, Timothy Osadolor, ya zargi majalisar dokoki da kokarin kara lokaci ga gwamnatin Tinubu.
Ya ce abin da ’yan Najeriya ke bukata ba wai matsar da zabe ba ne, sai dai tabbatar da cewa tsarin BVAS da isar da sakamakon zabe kai tsaye sun zama tilas cikin dokar zabe.
Shi ma kakakin jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya nuna damuwa cewa matsar da zabe gaba na iya cutar da jam’iyyun adawa da ke shirye-shiryen zaben 2027.
Ya ce:

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta cika baki kan tazarcen Tinubu a 2027

“Wadanda ke gwamnati za su fi kowa shiri, yayin da sauran jam’iyyu za su fuskanci kalubale wajen gyara tsare-tsarensu.”

Martanin shugabannin ADC da LP

Kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ba za ta yi tsokaci ba sai bayan ta ga cikakken kwafin kudirin da aka gabatar.

Sai dai kakakin tsagin jam’iyyar LP, Obiora Ifoh, ya nuna goyon baya ga shirin, yana mai cewa zai rage kashe kudi da kuma tashin hankali a lokutan zabe.

Kakakin jam'iyyar ADC
Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Legit ta tattauna da Amadu Mai Shago

A wata tattauna wa da Legit Hausa, Malam Amadu Mai Shago ya ce shi ma bai yarda da shirin dawo da zabe 2026 ba.

A cewarsa:


'Ba yadda za a yi mutane su yarda cewa an kulla gaskiya a kan dawo da zabe baya a lokacin da ko dokokin zaben da ake cewa za a gyara ba a yi ba."
'Ya kamata a bar zabe yadda ya ke a 2027 ba tare da sauyi ba."

2027: Ba a fara rajistar 'yan APC ba

Kara karanta wannan

Tinubu ya alakanta rashin tsaro da masu satar ma'adinai, ya yi kira ga duniya

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake cigaba da magana kan zaben 2027, jam'iyyar APC ta gaza fara rajistar mambobinta ta yanar gizo.

Binciken Legit Hausa ya nuna cewa an fara maganar fara rajistar 'yan APC ta yanar gizo ne a lokacin shugabancin Abdullahi Ganduje.

Wasu 'yan jam'iyyar APC sun bayyana cewa an gaza fara rajistar ne saboda sauyin shugabanci da aka samu da matsalolin cikin gida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng