Kusa a APC Ya Fadi Illar da Ficewar Farfesa Pantami Za Ta Yi Wa Jam'iyyar
- Akwai masu hasashen cewa tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, zai iya raba gari da jam'iyyar APC mai mulki a kasar nan
- Wani kusa a jam'iyyar ya nuna cewa ficewar Farfesa Pantami, za ta zama gagarumin koma baya ga APC a yankin Arewa da ma Najeriya gaba daya
- Khamis Darazo ya bada shawara ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da shugaban jam'iyyar APC na kasa kan matakin da ya kamata su dauka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Wani kusa a APC a jihar Bauchi, Khamis Darazo, ya nuna damuwa kan yiwuwar ficewar tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, daga jam’iyyar.
Khamis Darazo ya bayyana cewa ficewar Isa Ali Pantami daga APC babban rashi ne da zai shafi jam'iyyar musamman a Arewacin kasar nan.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Khamis Darazo ya bayyana ra’ayinsa ne a Bauchi ranar Lahadi yayin da yake tattaunawa da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara maganar ficewar Pantami daga APC
A yayin zantawar, ya roki fadar shugaban kasa da shugabancin jam’iyyar na kasa da su shiga tsakani cikin gaggawa bayan rahotannin da ke cewa Pantami na iya barin jam’iyyar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.
Ya yi gargadin cewa irin wannan lamari zai zama babbar asara ta siyasa da kuma koma-baya ga jam’iyyar APC a yankin Arewa da ma Najeriya gaba ɗaya.
Darazo ya nuna damuwa matuka kan jita-jitar da ke cewa Farfesa Pantami yana shirin barin jam'iyyar APC.
"Ya kamata fadar shugaban kasa da shugabancin jam’iyyar mu mai girma ta APC su kula da maganganun da ke yawo game da yiwuwar ficewar ɗan’uwa kuma dattijonmu, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, daga jam’iyyar.”
"Farfesa Pantami ba ɗan siyasa kaɗai ba ne, mutum ne mai ilimi, mai kawo sauyi, kuma mai haɗa kai, wanda kullum yake amfani da ilimi, addini da gaskiya wajen tallafawa gwamnati da kuma zaburar da matasan Najeriya.”
- Khamis Darazo
Wane gargadi Khamis Darazo ya yi?
Ya yi gargadin cewa rasa Pantami zai raunana jam’iyyar, tare da sare gwiwoyin matasa da dama a Najeriya da ke kallonsa a matsayin mutum mai gaskiya da hangen nesa.

Source: Facebook
Khamis Darazo ya kammala da yin kira ga Shugaba Bola Tinubu, shugaban APC na kasa, da sauran manyan jagorori su tattauna da Pantami domin warware duk wata damuwa ko rashin fahimta da zai iya zama sanadiyyar ficewarsa.
Tsohon minista ya magantu kan ficewa daga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Muazu Jaji Sambo, ya bayyana matsayarsa kan ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Muazu Jaji Sambo wanda ya yi minista a lokacin mullkin tsohon shuganan kasa marigayi Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa zai ci gaba da zama daram a jam'iyyar APC.
Tsohon ministan ya kuma bada tabbacin cewa yana goyon bayan manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a kokarin da yake yi na farfado da tattalin arzikin kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

