Gwamna Sule Ya Fadi Kalar Dan Takarar da Yake Son Ya Gaji Kujerarsa, Ya Ja Kunne

Gwamna Sule Ya Fadi Kalar Dan Takarar da Yake Son Ya Gaji Kujerarsa, Ya Ja Kunne

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa zai bayyana wanda yake so ya gaje shi a 2027 a fili, ba tare da tsoro ba
  • Ya gargadi masu mukaman siyasa a jiharsa da su daina bin ‘yan takara kafin lokacin ya yi, yana mai cewa ba zai lamunci haka ba
  • Gwamnan ya ce zaɓinsa ba zai dogara da son kai ko riba ba, sai dai wanda yake da ƙwarewa da hangen nesa wajen ci gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa — Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya yi magana game da magajinsa yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Gwamna Sule ya bayyana cewa idan lokacin ya yi, zai fito a fili ya bayyana wanda yake son ya gaje shi a 2027, yana mai cewa ba zai ji tsoron bayyana ra’ayinsa ba.

Kara karanta wannan

Daga faduwa zaben cike gurbi, dan takarar jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC

Gwamna ya magantu kan wanda zai gaje shi a 2027
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a gidan gwamnati. Hoto: Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Gwamna ya magantu kan magajinsa a Nasarawa

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a taron wayar da kai na yini ɗaya ga masu mukaman siyasa a jiharsa da aka gudanar a Lafia, cewar The Nation.

Sule ya bayyana cewa ba zai taba boye wanda yake son ya gaje shi ba inda ya tabbatar da cewa zai bayyana a fili.

Ya ce:

“Idan lokacin ya yi, zan fada a fili, wannan shi nake so, kuma zan bayyana dalilina. Duk wanda yake tunanin wani zai zo ya ce min ‘Sule, dole ka yi haka’, wannan mutum yana bukatar a kai shi asibitin mahaukata."

- Gwamna Sule.

Ya bayyana cewa yana da mutane a zuciya da yake ganin sun cancanci wannan kujera, amma yanzu bai yanke shawara ba, saboda lokaci bai yi ba.

Gwamna ya fara magana kan magajinsa a Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Gwamna Sule ya gargadi masu neman takara

Gwamna Sule, wanda ke kan wa’adinsa na biyu bayan lashe zaben 2023, ya ce ba zai nuna son kai ba, domin ba ya neman kuɗi, gida ko motoci daga wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan

Malami ya yi hasashen mai nasara a zaben 2027, ya ce gwamna zai taka wa Tinubu birki

Ya kara da cewa:

“Na ga wasu daga cikinku kuna bin ‘yan takara daban-daban. Ina so ku sani, duk wanda na gani tare da wani ɗan takara kafin lokaci ya yi, ranan nan na kore shi.
“Ba zan zabi wanda zai ba ni gida ko kuɗi ba. Ina so ne da mu samar da wanda zai iya jan masu zuba jari tare da ci gaba da ayyukan cigaba da muka fara a Nasarawa.”

Sai dai ya ce bai gama yanke hukunci ba kan wanda zai goyi bayansa, yana mai cewa duk labaran da ake yadawa cewa yana goyon bayan wani takamaiman mutum “labaran banza ne kawai.”

A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa ‘yan takara kusan 28 sun nuna sha’awar tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ciki har da Sanata Aliyu Ahmed Wadada, Akanta Janar Dr Musa Ahmed Mohammad, da tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu.

Gwamna Sule ya magantu kan matsalar tsari

Kara karanta wannan

Karfin hali: Gwamnan Oyo ya tsara yadda za a yi mulki a jiharsa bayan sauka a 2027

Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi na samun kudade masu kauri daga asusun tarayya.

Abdullahi Sule ya nuna cewa kudin da ake samu a yanzu sun ninka wadanda gwamnatocin Najeriya suke rabawa a shekarun baya.

Bisa hakan ne ya shawarci gwamnonin Arewa su maida hankali wajen magance matsalar rashin tsaro da ya fitini al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.