Amupitan: NNPP Ta Fadi Matsayarta kan Sabon Shugaban INEC yayin da Ake Maganganu
- Jagoran NNPP, Dr. Boniface Aniebonam, ya bayyana matsayar jam'iyyar bayan Bola Tinubu ya zabi sabon shugaban INEC
- Aniebonam ya nuna goyon bayansa ga zaben Farfesa Joash Amupitan da Bola Tinubu ya yi a matsayin shugaban hukumar da jero dalilansa
- Wanda ya kafa jam'iyyar ya ce babban aikin Amupitan shi ne gyara sunan INEC da dawo da amincewar ‘yan Najeriya da hukumar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ikeja, Lagos — Wanda ya assasa jam’iyyar NNPP, Dr. Boniface Aniebonam, ya yi magana kan batun nadin sabon shugaban hukumar INEC.
Aniebonam ya bayyana cikakken goyon bayansa ga zaben Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta kasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Source: Facebook
Matsayar NNPP kan sabon shugaban INEC
Aniebonam ya bayyana matsayinsa ne a ranar Lahadi a garin Lagos, bayan samun ce-ce-ku-ce kan nadin Amupitan, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Amupitan: Lauyoyi na shirin kawo cikas ga tabbatar da nadin shugaban INEC a majalisa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nadin, wanda zai maye gurbin tsohon shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, yana jiran amincewar majalisar dattawa kafin ya fara aiki.
Aniebonam ya ce Amupitan yana da babban aiki a gabansa tun daga yanzu, yana mai cewa:
“Abu na farko da ke gaban Amupitan shi ne gyara sunan hukumar INEC da kuma dawo da amincewar ‘yan Najeriya gare ta.
"Hukumar ta dade tana fuskantar rashin amincewa daga jama’a, don haka ya kamata ya maida hankali wajen gyara kuskuren baya.”

Source: Twitter
NNPP ta yabawa Tinubu kan nadin shugaban INEC
Ya kuma ce Bola Tinubu da Majalisar Zartarwa sun yi nazari sosai kafin zaben Amupitan, ya ce hakan na nuna shugaban na da niyyar gyara kura-kurai da suka dabaibaye ƙasa, musamman daga cikin INEC.
Aniebonam ya tuna cewa jam’iyyar NNPP ta taba samun rikicin cikin gida wanda ya nuna irin raunin hukumar INEC a lokacin tsohon shugaban ta, inda ya ce:

Kara karanta wannan
Da gaske sabon shugaban INEC na cikin lauyoyin Tinubu a zaben 2023? an samu bayanai
“A wannan lokaci Najeriya tana bukatar shugabanni masu ƙarfin hali da basira wajen yanke shawarar da ta dace domin sake gina ƙasar.
“Tsohon shugaban INEC ya yi biris da umarnin kotu da ya bukaci hukumar ta sabunta shugabancin NNPP na yanzu a cikin bayananta, wanda hakan ya zama abin kunya ga tsarin mulkin dimokuraɗiyya.”
Ya kara da cewa akwai batutuwa masu muhimmanci da sabon shugaban INEC zai fara dubawa shi ne binciken dalilin da ya sa aka yi watsi da hukuncin kotu, da kuma dawo da mutunci ga hukumar.
Aniebonam ya ce wannan abu babbar barazana ce ga tsarin jam’iyyu a Najeriya, domin hakan na iya bai wa wani damar canza tambarin jam’iyyar APC, PDP ko LP ba tare da izini ba, kamar yadda Punch ta kawo.
An musanta alakar Amupitan da Tinubu
Kun ji cewa babban Lauya a Najeriya ya yi karin haske kan cewa sabon shugaban INEC, Joash Amupitan na da alaka mai karfi da shugaban kasa, Bola Tinubu.
Lauya, Babatunde Ogala ya karyata cewa Amupitan yana cikin tawagar lauyoyin Bola Tinubu a kotun zaɓe wanda ake ta yadawa a kafofin sadarwa.

Kara karanta wannan
An gano tsofaffin shugabannin Najeriya 3 da ba su halarci taron majalisar koli ba
Ogala ya kalubalanci masu yaɗa jita-jita su fitar da hujja da za ta tabbatar da cewa sabon shugaban INEC ya yi aiki a wannan tawaga domin kare Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng