'Shirin da Ake Yi na Kifar da Tinubu cikin Watannin Nan idan Bai Yi Hankali ba'
- Shahararren Fasto mai hasashe kan siyasa ya sake fitar da wasu bayanai masu ban tsoro kan Bola Tinubu a cikin yan watannin nan
- Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Tinubu cewa wasu manyan mutane a Najeriya na shirin kifar da gwamnatinsa ba tare da bin ka'ida ba
- Ayodele ya ce wasu jami’an soji, ciki har da na Rundunar sojojin Ruwa, Sama da Ƙasa, na iya shiga cikin wannan shirin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya sake gargadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Malamin ya ce wasu mutane masu ƙarfi na shirin kifar da shi ba bisa doka ba inda ya ba shi wasu shawarwari.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da Tribune ta samu daga mai taimaka masa, Osho Oluwatosin, ya fitar a yau Lahadi 12 ga watan Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC: Gargadin da Fasto ya yi ga Tinubu
Ko a makon da ya gabata sai da malamin ya gargadi Tinubu game da hasashen da ya yi cewa wasu gwamnoni za su dawo APC.
Babban malamin addinin Kirista, Elijah Ayodele ya yi hasashe mai ban mamaki game da wasu gwamnonin adawa da za su iya komawa APC.
Malamin ya gargadi ga Bola Tinubu cewa wasu gwamnonin adawa za su koma APC amma ba duka ne ke son taimaka masa.
Limamin ya ce wasu daga cikinsu za su shiga jam’iyyar ne kawai don su sami albarkar shugaban ƙasa da kuma neman mukamai.

Source: Twitter
Shawarar Ayodele ga Ribadu, Hafsan tsaro
Ayodele ya bukaci Nuhu Ribadu, DSS, da Babban Hafsan Sojoji su kasance masu taka-tsantsan kan lamarin.
“Za a yi yunƙurin kifar da Tinubu ta hanyar da ba ta kundin mulki ba. NSA, DSS, da COAS su kula. Ana shirin tsakanin Nuwamba da Janairu."
- Elijah Ayodele
Fasto Ayodele ya ce wasu jami’an Rundunar sojojin Ruwa, Sama, da Sojojin Ƙasa za su shiga cikin lamarin, yana gargadin shugaban ya ƙarfafa tsaronsa sosai.
Fasto ya yabawa shugabannin hukumomin tsaro
Haka kuma, ya ce Najeriya na da Daraktan DSS da Babban Hafsan Soja masu ƙwazo da za su iya hana wannan yunƙuri idan aka ba su kulawa.
Ya kara da cewa:
“Ko Rundunar sojojin Ruwa da Sama za su shiga ciki, har da Sojojin Ƙasa. Tinubu ya shirya komai, ya canja dabarar tsaronsa.
“Muna da DSS DG mai ƙwazo, da COAS mai jarumtaka, za su iya dakile shirin. Shugaba ya saurari shawararsu kuma ya kula da su."
Fasto ya gargadi Tinubu game da lafiyarsa
A wani labarin mai kama da wannan, Elijah Ayodele ya yi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu game da wasu yan Arewa saboda zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.
Faston ya ce akwai wasu manyan Arewa da ke kokarin tumbuke shi a 2027 saboda matsalolin tattalin arziki da yunwa.
Babban malamin kiristan ya ce ya guji dogaro da 'yan amshin shata domin za su cutar da shi, kuma ya nemi masu tsoron Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


