Gwamnoni 3 na Shirin Shiga APC, Gwamna Bala Ya Yi Magana kan Masu Ficewa daga PDP
- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce matsorata ne ke barin jam'iyyar PDP saboda rikicin cikin gida da ake kuka da shi
- Shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya bukaci 'ya'yan jam'iyyar su zama masu juriya kuma kada su damu da masu sauya sheka
- Bala Mohammed ya kuma jaddada cewa babban taron PDP na kasa na nan kamar yadda aka shirya shi a Ibadan, babban birnin Oyo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya soki masu shiri da wadanda suka bar jam'iyyar adawa.
Gwamna Bala ya bayyana cewa wadanda ke barin jam’iyyar PDP saboda ayyukan wasu bara gurbi da rikicin cikin, a matsayin matsorata kuma marasa kwarin gwiwa.

Source: Twitter
Leadership ta ruwaito cewa Bala Mohammed ya kuma tabbatar da cewa taron PDP da aka shirya gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo, ranar 15 ga Nuwamba, na nan daram ba sauyi.

Kara karanta wannan
An fara guna guni da Majalisar Benue ta amince gwamna ya karbo bashin Naira biliyan 100
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na gangamin APC da za a yi a Ibadan.
Gwamnoni 3 da ake zargin za su bar PDP
Wannan kalamai na zuwa ne yayin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya shirya ficewa daga jam’iyyar PDP a hukumance mako mai zuwa.
Haka kuma ana hasashen cewa Gwamna Douye Diri na Bayelsa da Gwamna Agbu Kefas na Taraba ma za su biyo bayansa nan ba da jimawa ba.
Tun farkon wannan shekara, Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta suka fice daga PDP zuwa APC.
Gwamma Bala ya soki masu ficewa daga PDP
Sai dai Gwamna Bala Mohammed ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su kasance masu karfin guiwa, kada su bari ficewar wasu ta raunana su, yana mai cewa:
“Ku kasance da kwarin gwiwa, kada ku damu da wadanda ke ficewa. Ku tsaya, ku nuna jarumtar ku, zama kan abu daya ke nuna mutum na da gaskiya.
"Amma barin jam’iyya saboda mutum daya ko mace daya, alamar rashin jarumta ce. Ku nuna kuna da karfin hali da jajircewa.”

Source: Facebook
Shin an samu sauyi a shirin taron PDP?
Daily Trust ta rahoto cewa yayin da yake tabbatar da cewa taron gangamin PDP zai gudana kamar yadda aka tsara, Bala Mohammed ya ce:
“Mun sha wahala sosai a jam’iyya, amma mun jure kuma mun tsallake. Wannan gangami zai gudana, kuma za mu tafi Ibadan, in sha Allahu. Babu wani karfi ko iko da zai hana mu.
Sanatan Bauchi ya fice daga jam'iyyar PDP
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Samaila Dahuwa Kaila, wanda ke wakiltar mazabar Bauchi ta Arewa a Majalisar Dattawa ya fice daga jam'iyyar PDP.
Sanata Samaila ya danganta matakin da ya dauka na barin PDP da rikice-rikicen cikin gida da suka ki karewa a jam’iyyar.
A wasikar da ya aike wa shugabannin PDP, Sanatan ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne bayan tattaunawa da magoya baya da abokansa na siyasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
