Da Gaske Sabon Shugaban INEC na cikin Lauyoyin Tinubu a Zaben 2023? An Samu Bayanai

Da Gaske Sabon Shugaban INEC na cikin Lauyoyin Tinubu a Zaben 2023? An Samu Bayanai

  • Babban Lauya a Najeriya ya yi karin haske kan cewa sabon shugaban INEC, Joash Amupitan na da alaka mai karfi da shugaban kasa, Bola Tinubu
  • Lauya, Babatunde Ogala ya karyata cewa Amupitan yana cikin tawagar lauyoyin Bola Tinubu a kotun zaɓe wanda ake ta yadawa a kafofin sadarwa
  • Ogala ya kalubalanci masu yaɗa jita-jita su fitar da hujja da za ta tabbatar da cewa sabon shugaban INEC ya yi aiki a wannan tawaga domin kare Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An yi ta yada jita-jitar cewa sabon shugaban INEC da aka zaba, Farfesa Joash Amupitan yana da kyakkyawar alaka da Bola Tinubu.

Wani fitaccen lauya Babatunde Ogala (SAN) ya yi karin haske kan jita-jitar da ake yadawa wanda ya fara sanya shakku kan nadin nasa.

Kara karanta wannan

Amupitan: Lauyoyi na shirin kawo cikas ga tabbatar da nadin shugaban INEC a majalisa

An karyata alakar Tinubu da sabon shugaban INEC
Sabon shugaban INEC, Joash Amupitan da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @DOlusegun.
Source: Twitter

Rahoton TheCable ya ce Ogala ya karyata cewa Joash Amupitan, ya kasance cikin tawagar lauyoyin da suka kare Bola Tinubu a kotun zaɓe a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: Dalilin zaben Amupitan ya rike INEC

Hakan ya biyo bayan zabin Amupitan domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu da ya ajiye aiki bayan cikar wa'adinsa.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana bayan dauko sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC domin ci gaba daga inda Farfesa Yakubu ya tsaya.

Tinubu ya bayyana cewa ya zabi Joash Amupitan ne saboda gaskiyarsa, rashin shigar sa cikin siyasa, da kuma kyakkyawan tarihi.

Farfesa Amupitan shi ne mutum na farko daga Jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya da aka taba nada wa mukamin shugaban hukumar ta INEC.

Ana zargin alaka mai karfi tsakanin Tinubu da sabin shugaban INEC
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ana yada 'alakar' Tinubu da shugaban INEC

Lauyan ya tabbatar da cewa wannan magana ƙarya ce, babu wata hujja da ke tabbatar da hakan inda ya kalubalanci masu yada ta, ya ce an yi ne kawai domin kawo tarnaki.

Kara karanta wannan

'Babban dalilin da ya sa na zabi Amupitan, shugaban INEC': Tinubu ya fadi hikimarsa

Ogala ya ce:

“Ban taɓa ganin sunansa cikin lauyoyin da suka kare shugaban ƙasa ba. Idan wani yana da hujja, to ya fito da ita a fili.”

Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan ƙarya da ke iya tayar da rikici wanda zai kawo shakku kan sahihancin nadin nasa, cewar rahoton The Nation.

Bincike ya nuna cewa babu inda aka ambaci sunan Amupitan a cikin takardun hukuncin kotun zaɓe ko na kotun koli, inda hakan ya tabbatar da cewa bai kasance cikin tawagar lauyoyin Tinubu ba.

ADC ta ba sabon shugaban INEC, Amupitan shawara

Mun ba ku labarin cewa bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ADC ta yi martani.

Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi hannunka mai sanda ga shugaban na INEC biyo bayan nadin da aka yi masa domin jan hankalinsa game da adalci.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, Shugaba Tinubu ya gabatar da sunan sabon shugaban INEC na kasa

Mai magana da yawun ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa Farfesa Amupitan zai iya sanya sunansa a cikin tarihi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.