Adadi Ya Karu: Gwamnoni 3 Sun Shirya Komawa Jam'iyyar APC Mai Mulkin Najeriya
- Alamu na nuna cewa jam'iyyar APC za ta samu karin gwamnoni uku da za su baro tsagin adawa zuwa cikinta a mako mai zuwa
- Rahotanni sun gano sunayen gwamnoni biyu daga ciki, wadanda za su sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya
- Zuwa yanzu dai APC na da gwamnoni 23 kuma idan wannan sauya sheka ta tabbata, adadin zai karu yayin da na PDP za su ragu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu - Matukar ba a samu wani jinkiri ko sauyi ba, rahotanni sun nuna cewa gwamnonin jihohi uku za su bar jam'iyyun adawa zuwa APC mai mulkin kasa.
Rahotanni daga majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa gwamnonin za su jagoranci mukarrabansu da 'yan Majalisar jihohinsu zuwa APC a makon gobe.

Source: Facebook
Wasu gwamnoni ne za su koma APC?
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa daga cikin waɗanda ake tsammani za su koma APC akwai Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu da Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Sai kuma gwamna na uku wanda rahoton ya nuna cewa an boye sunansa, har yanzu ba a bayyana ba.
Gwamna Mbah ya samu goyon bayan manyan jiga-jigan PDP a jihar Enugu kan batun komawa APC, yayin da a Bayelsa kuma, Diri ke fuskantar kalubale daga wasu yan majalisar tarayya.
Gwamna Mbah ya samu hadin kan 'yan PDP
Wani hadimin Gwamna Mbah da aka tuntuba a jiya ya ce, “Ba zan iya tabbatarwa ko musanta batun ba,” amma daga bisani ya dawo ya ce, “komawar gwamnan zuwa APC ta tabbata, amma ba a sa rana ba.”
Idan Gwamna Mbah ya jagoranci wannan sauya sheka, to hakan na iya girgiza PDP, domin kusan gaba daya jagororin jam'iyyar za su bi shi zuwa APC, in ji The Nation.
A jihar Bayelsa kuwa, rahotanni sun nuna cewa Gwammna Diri ya dade yana shirin sauya sheka zuwa APC, kuma ana sa ran zai cika burinsa a mako mai zuwa.
Majiyoyi sun ce tuni Gwamna Diri ya tuntubi tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da wasu dattawan jihar kafin yanke shawarar barin PDP, yanzu kuma ya samu goyon bayan ‘yan majalisar dokokin Bayelsa.
Kalubalen da Gwamna Diri ke fuskanta
Sai dai kuma, da yawa daga cikin ‘yan majalisar tarayya daga jihar sun ki amincewa da wannan mataki, suna cewa babu wani dalili mai ƙarfi da zai sa a koma APC.
A cewar rahoton, Sanata Seriake Dickson (Bayelsa ta Yamma), Sanata Benson Agadaga, da ’yan majalisar wakilai uku cikin biyar, ba za su bi Diri zuwa APC ba.
Duk da haka, wasu na kusa da gwamnan sun tabbatar da cewa ya riga ya yanke shawara, inda ɗaya daga cikin su ya ce:
“Ba za mu koma baya ba, an wuce matakin shawara. Gwamna zai koma APC tare da wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar, duk da dai ba kowa ba.
"Haka kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya za su bishi, ciki har da Sanata Konbowei Benson.”

Source: Twitter
Wani jigo a APC, Usman Abdullahi ya shaida wa Legit Hausa cewa jam'iyyar za ta ci gaba da fadada daga nan har zaben 2027.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 3 na shirin shiga APC, Gwamna Bala ya yi magana kan masu ficewa daga PDP
A cewarsa, dawowar wadannan gwamnonin APC zai kafa tarihi a siyasar Najeriya musamman yankim Kudancin Najeriya.
Kwamared Usman ya ce:
"APC ta wuce duk yadda kuke tunani, kuma ba wai muna kokarin maida kasar ta jam'iyya daya bace, ko kadan ba mu hana yan adawa gina kansu ba, amma muna kokarin fadada jam'iyya tun daga sama har kasa.
"Idan ka duba tarihin Najeriya, tun daga 1999 zuwa yau ba a taba samun wata jam'iyya da ba PDP ba, da ta karbe mulkin jihohi da yawa a Kudu, amma yanzu ka duba, mu da su wa ya fi yawan gwamnoni a Kudu?"
Sanata daga Enugu ya koma APC
A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Kelvin Chukwu ya tabbatar da sauya shekarsa hukumance daga LP zuwa APC mai mulki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Kelvin Chukwu ga sauran abokan aikinsa.
Sanata Chikwu ya bayyana cewa ya zabi barin LP ne saboda rigingimun da suka addabe ta kuma yana ganin zai fi cika muradan mutanensa a APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
