Gwamna na Shirin Komawa APC, Tsohon Jagora a Majalisar Dattawa Ya Fice daga PDP

Gwamna na Shirin Komawa APC, Tsohon Jagora a Majalisar Dattawa Ya Fice daga PDP

  • Jam'iyyar PDP na ci gaba da rasa manyan jiga-jiganta yayin da babban zaben shekarar 2027 ke kara kusantowa
  • Tsohon Mataimakin Mai Tswatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Agboola Ayoola, wanda aka fi sani da Alleluyah, ya fice daga PDP
  • Ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda yana shirin canza akalar siyasarsa, ya kuma yi wa jam'iyyar PDP fatan alheri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Tsohon Mataimakin Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Agboola Ayoola, wanda aka fi sani da Alleluyah, ya fice daga jam’iyyar PDP a jihar Oyo.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu labarin cewa Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu zai bar PDP ya koma APC a makon gobe.

Jam'iyyar PDP.
Hoton wasu mambobin PDP su na daga tutocin jam'iyyar a wurin taro. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ce Ayoola, ɗan asalin ƙaramar hukumar Itesiwaju, ya sanar da murabus saga PDP ne wata wasika da ya rubuta ranar Juma’a, 10 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Gwamna ya tsallake da APC ta hana manyan 'yan siyasa 2 shiga takara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ayoola ya rike kujerar Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu a ƙarƙashin tsofaffin gwamnonin jihar, Rashidi Ladoja da marigayi Adebayo Alao-Akala, tsakanin 2003 zuwa 2011.

Daga baya kuma, ya zama sanata ɗaya tilo da jam’iyyar PDP ta samu daga yankin Kudu maso Yamma tsakanin 2011 zuwa 2015.

Me yasa Sanata Ayoola ya bar PDP?

A cikin wasikar ficewarsa da ta shiga hannun yan jarida ranar Juma’a, Ayoola ya yi godiya ga jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi ya yi hidima ga jama’a a matakan jiha da ƙasa.

Ya ce dalilin ficewarsa daga PDP ya samo asali ne daga shirye-shiryen siyasa da ya kudiri a aniyar yi a gaba, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Sannan ya kuma bayyana cewa rashin ganinsa a tarukan jam’iyyar PDP a baya-bayan nan ba abin mamaki ba ne, domin akwai wasu shirye-shirye da yake yi.

Tsohon Sanatan ya mika takardar fita daga PDP

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

A wasikar, tsohon jagora a Majalisar Dattawan ya ce:

“Ni, Sanata Agboola, wanda ke matsayin mamba kuma jagora a matakin jiha da ƙasa, ina gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba ni na yi aiki da kuma nasarorin da muka samu tare.
"Duk da haka, idan kuka lura, ban halarci tarukan jam’iyyar da aka gudanar kwanan nan ba, hakan ta faru ne saboda shirye-shiryen siyasa na gaba da suka zama wajibi gare ni a wannan lokaci.
"Saboda haka, ina sanar da ficewa ta daga jam’iyyar PDP daga ranar 10 ga Oktoba, 2025, sannan ina yi wa PDP fatan nasara a dukkan harkokin da ta sa a gaba."
Sanata Agboola Ayoola.
Hoton tsohon sanata daga jihar Oyo, Agboola Ayoola. Hoto: Agboola Ayoola
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Benue ya bar PDP?

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Torwua Suswam ya karyata rahoton da aka fara yadawa cewa ya bar PDP zuwa APC.

Suswam, ta bakin mai magana da yawunsa, Bede Bartholomew ya ce yana nan daram a jam'iyyarsa ta PDP kuma ba shi da shirin sauya sheka.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Gabriel Suswam ya tabbatar da cewa ya amsa gayyatar gwamnan Benue, Hyacinth Alia, na halartar taron liyafa da aka shirya a gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262