Malami Ya Yi Hasashen Mai Nasara a Zaben 2027, Ya Ce Gwamna Zai Taka Wa Tinubu Birki
- Fitaccen Fasto daga kasar Kamaru ya yi hasashen abin da zai faru a zaben shekarar 2027 da za a fafata da Shugaba Bola Tinubu
- Fasto Boris Jedidiah ya ce Tinubu zai sake lashe zaben shugaban ƙasa a 2027 saboda hakan nufin Allah ne amma zai fuskanci kalubale
- Malamin ya bayyana cewa wani gwamna daga Najeriya zai yi takara amma Tinubu ne za a sanar a matsayin wanda ya yi nasara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yaounde, Cameroon - Shahararren Fasto, Boris Jedidiah ya yi wani irin hasashe game da zaben shekarar 2027 da ke tafe a Najeriya.
Faston da ke Kamaru ya yi hasashen cewa sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 al’amari ne da Allah ya ƙaddara tun farko.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na YouTube a jiya Alhamis 9 ga watan Oktobar shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan
'Mu fa sai Jonathan,' : Kungiyar Arewa ta dage tsohon shugaban kasa ya sake takara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto ya yi hasashen zaben 2027 a Najeriya
Fasto Jedidiah ya bayyana cewa wani gwamna daga Najeriya zai tsaya takarar shugaban ƙasa, amma ba zai yi nasara ba, domin Shugaba Tinubu ne zai ci zaben.
A cewar malamin, duk wani gwamna a Najeriya da zai yi adawa da mulkin Tinubu yana sabawa nufin Allah ga ƙasar nan.
A kalamansa, ya ce:
“Ubangiji ya nuna mani cewa wannan gwamna ba zai zama shugaban ƙasa ba. Mai girma Bola Ahmed Tinubu ne zai zama shugaban ƙasa a zaben 2027.
“Lokacin zaben shugaban ƙasa na Najeriya a shekarar 2027, wani gwamna daga cikin jihohin ƙasar zai tsaya takarar shugaban ƙasa.
"Amma Ubangiji ya faɗa mani cewa wannan gwamna ba zai zama shugaban ƙasa na Najeriya ba, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ne za a ayyana a matsayin shugaban ƙasa na Najeriya a zaben 2027.”

Source: Facebook
Martanin wasu mutane kan hasashen zaben 2027

Kara karanta wannan
Sanatan APC ya kafa misali da Trump, ya ce da yiwuwar ya zama shugaban Najeriya a 2039
Wannan bidiyo ya jawo maganganu da martanin al'umma musamman daga Najeriya duba da cewa Faston ya fito ne daga Kamaru da ke makwabtaka da kasar.
Wasu daga ciki sun nuna damuwa game da sake dawowar Bola Tinubu musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki.
@AnthonyAchebe-vf1ty:
"Shin ya yi nasara a karon farko, Ubangiji ne ya fada maka cewa ya yi nasara ko kuma kawai da karfi ya kwace ya gudu.
"Abin da ya kamata shi ne ka ba da karfi wurin ci gaba da ayyukanka da kake yi, ka watsar da maganar siyasa."
@alloysusike9384:
"Ka sake dawowa ko.?"
@pauldrums4081"
"Tinubu kuma har yanzu!!!."
Fasto a Kaduna ya yi hasashen zaben 2025
Mun ba ku labarin cewa malamin addini daga Kaduna ya bayyana wani mafarki da ya yi mai ban tsoro musamman game da zaben shugaban kasa a Najeriya.
Matashin Faston, Godwin Auta Musa, ya ce ya samu wahayi cewa zaben 2027 zai yi kama da zaben 12 ga watan Yuni na shekarar 1993.
Ya ce cikin mafarki ya ga 'dan takara ya yi nasara amma gwamnati ta soke sakamakon, yana kira ga ‘yan kasa su tashi tsaye da addu’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng