Boye Boye Ya Kare: Gwamna Ya Gama Shiri, Zai Sauya Sheka zuwa APC Ranar Talata
- An shirya tarbar Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ranar Talata, 14 ga watan Oktoba, 2025
- Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye ne ya sanar da hakan yayin hira da manema labarai a Abuja
- An jima ana rade-radin cewa Gwamna Mbah, wanda ya samu nasarar hawa mulki a inuwar PDP a zaben 2023, zai koma jam'iyyar APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Rahotanni masu karfi sun tabbatar da cewa Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu da mukarrabansa za su sauya sheka daga PDP zuwa APC a mako mai zuwa.
Bayanai sun ce an kammala dukkan shirye-shirye kuma Gwamna Peter Mbah, zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa APC za ta karbi mai girma gwamnan ne a wani taro da aka shirya a birnin Enugu, babban birnin jihar ranar Talata mai zuwa.
Gwamna Mbah ya gama shirin komawa APC
Rahotanni sun nuna cewa Mbah zai shiga jam’iyya mai mulkin Najeriya ne tare da wasu ’yan majalisar dokoki na jihar Enugu da na tarayya.
Haka kuma ana sa ran Gwamna Mbah zai taho tare da mambobin majalisar zartarwa ta jiha, da shugabannin jam’iyyar PDP na matakin gunduma da ƙananan hukumomi zuwa APC.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, tare da mataimakinsa daga kudu, Hon. Emma Eneukwu, sun kaddamar da kwamitin rikon kwarya mai mutum bakwai a jihar Enugu.
APC ta sanar da shirin karbar Gwamna Mbah
Yayin kaddamar da kwamitin rikon, sun bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙari don ƙarfafa tasirin jam’iyyar APC a yankin kudu maso gabas.
Sabon shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya tabbatar da cewa suna shirin tarbar Gwamna Mbah da mukarrabansa.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
Dr. Nwoye ya sanar da haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar APC da ke Abuja bayan rantsar.da su.
Shugaban APC na Enugu ya ce jam'iyyar za ta tarbi mai girma gwamnan tare da duka mutanensa da suka sauya sheka a hukumance a ranar 14 ga Oktoba, 2025.
A ranar Alhamis da ta gabata ne kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na APC ya rushe shugabannin APC na jihar Enugu tare da naɗa sabon kwamitin rikon kwarya mai mutum bakwai.
Sanata ya yi maganar nadin ministoci
An ji labari Muhammad Ali Ndume ya ce ba aikin majalisar dattawa ba ne binciken sunayen ministocin da shugaban kasa ya turo masu.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar yankin Borno ta kudu ya fadi hakan yayin martani kan badakalar tsohon ministan tarayya, Uche Nnaji.
Kwanaki bayan Nnaji wanda ya fito daga Enugu ya yi murabus, Ndume ya ce DSS ke da alhakin tantance ministoci tare da bincike kan takardunsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
