Karfin Hali: Gwamnan Oyo Ya Tsara yadda za a Yi Mulki a Jiharsa bayan Sauka a 2027
- Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana iya zaɓar wanda zai gaje shi daga cikin jami'ansa a 2027
- Ya bayyana cewa hakan zai tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan da gwamnatinsa ta fara shimfidawa
- Seyi Makinde ya ce karshe dai ‘yan jihar ne za su yanke hukunci kan wanda zai zama gwamna bayan sa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo – Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana yiwuwar cewa wanda zai gaje shi a zaben shekarar 2027 zai fito ne daga cikin tawagarsa ta yanzu.
Makinde ya ce wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da dorewar ci gaban da gwamnatinsa ta shimfiɗa tun bayan da ta hau mulki.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi kan kasafin kuɗin 2026 a Jami’ar Ibadan.

Kara karanta wannan
An fara guna guni da Majalisar Benue ta amince gwamna ya karbo bashin Naira biliyan 100
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani rahoto na Business Day ya ce Makinde ya yi maganar ne yayin da ake kiransa ya kara da Bola Tinubu a zaben 2027.
Wa zai zama gwamnan Oyo a 2027?
Seyi Makinde ya ce yana ganin ya dace wanda zai gaje shi ya fito daga cikin tawagar da ke aiki da shi yanzu.
Gwamnan ya fadi haka ne domin a cewarsa, sun riga sun fahimci manufofin gwamnatinsa da hanyoyin cigaba da aka tsara.
A cewarsa:
“Idan muka fito da mutum daga cikin tawagarmu, hakan yana nufin mun tantance shi kuma mun san yana da cikakken ilimi game da abin da muke yi.
An tsara yadda za a yi mulki a Oyo
Ya ƙara da cewa tuni gwamnatinsa ta tsara taswirar ci gaba wacce za ta tabbatar da dorewar ayyuka bayan shekarar 2027.
Seyi Makinde ya kara da cewa yana ganin mutanen da ke cikin tawagarsa sun riga sun fahimci taswirar sosai.

Kara karanta wannan
Malami ya yi hasashen mai nasara a zaben 2027, ya ce gwamna zai taka wa Tinubu birki
Tasirin 'yan jihar Oyo a zaben 2027
Sai dai Makinde ya jaddada cewa a karshe, hukuncin zaɓen wanda zai zama gwamna na gaba ba a hannunsa yake ba, yana hannun mutanen jihar Oyo.
The Guardian ta rahoto ya ce:
“Ko da mun fitar da wanda muke ganin ya dace, ‘yan jihar ne za su tantance su kuma su yanke hukunci.
"Lokacin siyasar nuna iko ya wuce a Oyo, yanzu mutane za su yi tambayoyi kafin su zaɓi shugabanni.”
Gwamnan ya bayyana cewa al’ummar jihar sun waye sosai wajen tantance abin da ya dace da makomar jiharsu, don haka ya kamata masu neman mulki su san da haka.

Source: UGC
Makinde ya nemi hadin kai a Oyo
Makinde ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da marawa gwamnati baya, tare da bayar da shawarwari don inganta ayyukan da ke gudana.
Ya ce burinsa shi ne ganin Oyo ta zama cibiyar tattalin arziki da ilimi a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Minista zai nemi gwamna a Oyo
A wani rahoton, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa zai nemi gwamna a jihar Oyo a 2027.
Ministan ya bayyana aniyarsa ne a wani taro inda ya yi ikirarin cewa lokacinsa na zama gwamna ya yi.
Adelabu na cikin ministocin shugaba Bola Tinubu da suka fito karara suka bayyana aniyarsu ta takarar gwamna a zabe mai zuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
