Manyan 'Yan Siyasan da Aka Ja Kunnensu kan Yin Takarar Shugaban Kasa a 2027
FCT, Abuja - An fara buga kugen siyasa yayin da Najeriya ke kara matsawa kusa da zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Source: Twitter
Kungiyoyin matsin lamba na siyasa da fitattun ‘yan kasa sun fara tattaunawa kan mutanen da ake ganin akwai yiwuwar su tsaya takara.
An bukaci wasu 'yan siyasa su hakura da takara
An fara kiraye-kiraye ga wasu manyan ‘yan siyasa da su janye daga fafutukar neman mulkin Najeriya a zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu masu irin wadannan kiraye-kirayen dai na maida hankali kan samun daidaito tsakanin yankuna, don mutunta tsarin karba-karba da ake amfani da shi a kasar nan.
1. Atiku Abubakar
Tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Atiku Abubakar.kan ka da ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Jaridar Daily Trust tace Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Atiku ya maida hankali kan goyawa matasa baya.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci jagoran 'yan adawa a Najeriya da ya mai da hankali kan zama uban al'umma.
2. Bala Mohammed
Wata kungiya mai suna Concerned PDP League (CPDPL), wacce ke cikin jam’iyyar PDP, ta shawarci gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed, da ka da ya yi takarar shugaban kasa a 2027.
Ƙungiyar ta gargade shi da ka da ya fara neman mulkin Najeriya har sai zuwa shekarar 2031.
Ta nuna cewa bayyana muradin neman yin takara tun da wuri na iya tayar da rikice-rikice a cikin jam’iyyar da tsarin siyasar kasa baki ɗaya.
CPDPL ta bayyana shawarar a matsayin wani mataki domin kare jam’iyyar daga rarrabuwar kai da kuma girmama ka’idar karba-karba tsakanin yankunan Najeriya.
Daga baya, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ya hakura da yin takarar shugabam kasa a 2027.
Jaridar The Nation ta ce Gwamna Bala ya bayyana cewa ya ajiye burinsa na neman shugaban kasa a gefe, domin ci gaban jam’iyyar PDP da haɗin kan Najeriya gaba ɗaya.
3. Goodluck Jonathan
'Yan siyasa da dama da wasu kungiyoyi sun yi kira ga Goodluck Jonathan, ka da ya nemi takarar shugaban kasa a 2027.
Jaridar The Punch ta ce tsohon dan takarar gwamnan Legas na jam'iyyar PDP, Abdul-Azaeez Adeniran ya gargadi Goodluck Jonathan da kada ya saurari masu cewa ya nemi takara a zaben 2027.
Ya ce tsohon shugaban kasan zai yi babban kuskure a siyasance idan ya tsaya takara, domin a cewarsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai doke shi a zaɓen 2027.
“Ina bada shawara ga Jonathan da kada ya sake shiga takarar shugaban kasa. Wadanda ke ba shi shawara, yaudararsa suke yi."
"Tinubu gogaggen ɗan siyasa ne, wanda Jonathan ko wani ɗan siyasa ba za su iya kayar da shi a 2027 ba."
- Abdul-Azeez Adeniran
Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya shawarci Jonathan ka da ya yi takara a zaben 2027.
A yayin wata hira da tashar Channels tv, Oshiomhole ya bukaci Jonathan ka da ya dauki shawarar masu matsa masa lamba kan sake neman shugabancin Najeriya.
4. Bola Ahmed Tinubu
A gefe guda kuma, tsohon mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya sake neman wa’adin mulki na biyu a 2027.

Source: Facebook
Yayin da yake magana a wani shiri na tashar Arise Television, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa lokacin Shugaba Tinubu ya kare, kuma ‘yan Najeriya za su nemi “dimokuraɗiyya ta gaskiya” a zabe na gaba.
“Ina tsammanin Tinubu zai janye daga takara. Idan shi ɗan siyasa ne mai hangen nesa, zai yi hakan."
- Yusuf Datti Baba-Ahmed
An shigar da karar hana Jonathan takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani lauya ya shigar da kara gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Lauyan mai suna Johnmary Jideobi ya shigar da karar ne don neman hana Jonathan yin takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan
"Ka saurari matarka": Kusa a APC ya ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu a 2027
Johnmary Jideobi ya nemi kotu ta bayar da umarnin da zai hana Jonathan gabatar kansa ga kowace jam'iyya don takarar shugaban kasa a 2027 ko nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

