Ana Jita Jitar Komawa ADC, Pantami Ya Sanya Labule da Shugaban PDP, an Ji Tattaunawarsu
- Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami na ci gaba da karbar bakuncin manyan 'yan siyasa a gidansa da ke Abuja
- Farfesa Pantami ya gana da shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Ambasada Umar Iliya Damagum a ziyararsa ta ban girma
- Majiyoyi sun ce Pantami da bakin nasa sun tattaunawa kan ci gaban ƙasa da al’amuran mulki, noma, tattalin arziƙi da sauransu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yayin da aka fara yada jita-jitar cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya koma jam'iyyar hadaka ta ADC, malamin ya gana da shugaban PDP.
Shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Umar Iliya Damagum ya ziyarci tsohon ministan sadarwa, Farfesa Pantami a birnin Abuja.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Farfesa Pantami ya wallafa a shafin Facebook da safiyar yau Juma'a 10 ga watan Oktobar 2025.
Rade-radin komawar Isa Pantami ADC
Wannan ganawar ta zo a daidai lokacin da wasu suka yi ta yadawa a kafofin sadarwa ciki har da Ahmed Tijjani Ramalan cewa Malam Isa Pantami ya bar APC zuwa ADC.
Hakan ya biyo bayan halartar wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ADC da Pantami ya yi a Abuja tare da Atiku Abubakar da David Mark da sauran jiga-jiganta.
Sai dai Legit Hausa ta yi bincike kan sahihancin komawar Pantami ADC inda ta gano babu inda tsohon ministan ya sanar da haka a hukumance har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.
Pantami ya gana da shugaban PDP a Abuja
A cikin rubutun da ya yi, Pantami ya bayyana farin cikinsa bisa karbar bakuncin shugaban PDP da kuma tawagarsa a gidansa da ke Abuja.
Pantami ya rubuta cewa:
"Jiya da dare, na karɓi bakuncin Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Mai girma Ambasada Umar Iliya Damagum, a gidana da ke Abuja.
"Tare da shi akwai ma’ajin jam’iyyar ta kasa, Alhaji Ahmad Yayari, tsohon Ministan Al’adu da yawon buɗe ido na Najeriya, Alhaji Muhammad Abubakar Sadiq.
Har ila yau, akwai tsohon darakta kuma ƙwararren masani a harkar kuɗi, Alhaji Bappa Ahmad Abdullahi."

Source: Facebook
Abubuwan da Pantami ya tattauna da Damagum
Farfesa Pantami ya bayyana cewa shi da Damagum da tawagarsa sun tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi noma da mulki.
Pantami ya ce kuma sun tabo batun tattalin arziki da bangaren ilimi da kuma abubuwan da suka shafi Arewacin Najeriya da hadin kan kasa.
A cewarsa:
"Mun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi mulki, noma, tattalin arziƙi, ilimi, yankin Arewa da kuma haɗin kan Najeriya baki ɗaya.
Ina matuƙar godiya da wannan ziyara da mai girma Ambasada da tawagarsa suka kawo, wanda ta ƙara tabbatar da zumunci da haɗin kai a tsakaninmu."
Shugaban APC ya gana da Pantami a Abuja
Mun ba ku labarin cewa shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyara gidan Farfesa Isa Ali Pantami a Abuja inda suka tattauna batutuwa da dama.
Pantami ya bayyana cewa sun shafe shekaru tare a jami’a lokacin da Nentawe ke yin digiri na biyu, inda suka tuna lokutan farin ciki.
A cewar Pantami, sun tattauna kan ilimi, tattalin arziki, mulki da kuma jana’izar mahaifiyarsa, yana mai godiya bisa wannan muhimmiyar ziyara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


