Mutanen da Suka Ja Kunnen Jonathan game da Sake Neman Mulkin Najeriya a 2027
Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan na cikin manyan 'yan adawar da ake tunanin za su nemi takara a zaben 2027 mai zuwa.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Duk da Jonthan bai fito karara ya nuna aniyarsa ta sake neman mulkin Najeriya ba, amma wasu da ake ganin suna da kusanci da shi sun ce zai dawo siyasa a 2027.

Source: Facebook
Jita-jitar takarar Jonathan a 2027 ta kara karfi
Jaridar Guardian ta ce jita-jitar ta kara karfi ne lokacin da Tsohon Ministan Yada Labarai, Farfesa Jerry Gana ya yi ikirarin cewa Jonathan zai nemi takara a zabe mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gana ya tabbatar da cewa Jonathan zai dawo ya sake neman shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Farfesa Gana ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaben shugabannin PDP na Jihar Neja a birnin Minna.
A cewarsa, ’yan Najeriya sun dandana mulkin wasu shugabanni biyu bayan Jonathan, kuma yanzu suna bukatar dawowarsa domin gyara halin da ake ciki.
"Ina tabbatar muku cewa Jonathan zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 a ƙarƙashin PDP, don haka mu shirya mu zaɓe shi ya dawo matsayin shugaban ƙasa.”
Jerin mutanen da suka ja kunnen Jonathan
Wannan kalamai dai sun ja hankalin yan Najeriya, inda wasu ke maraba da Jonathan idan ya amince zai nemi takara, wasu kuma suka gargade shi.
Legit Hausa ta tattaro maku wadanda suka ja kunnen Jonathan da kar ya yi kuskuren dawowa siyasa domin zai iya barar da ragowar mutuncinsa. Ga su kamar haka.
1. Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga
Bayan kalaman Jerry Gana, Fadar Shugaban Kasa ta gargadi Jonathan da kar ya rudu da mutane irinsu tsohon Ministan domin son zuciyarsu kadai suka sa a gaba.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce Jerry Gana yana ruɗar kansa da tunanin cewa Jonathan zai iya kayar da Shugaba Tinubu wanda ’yan Najeriya suka zaɓa a 2023.
"Gana ya yaudari kansa da yake ganin cewa tsohon shugaban ƙasa zai iya doke Shugaba Tinubu bayan shekaru 12,” in ji Onanuga.

Source: Twitter
A cewar rahoton Daily Trust, Onanuga ya kuma gargaɗi Jonathan da ya yi hattara da ’yan siyasa irin su Jerry Gana, yana mai cewa:
“Irin waɗannan ne masu dadin baki, waɗanda ke neman amfani da shi don cimma muradunsu na kashin kai ko na ƙabilanci," in ji shi.
2. Kenneth Okonkwo
Lauya kuma ɗan siyasa, Kenneth Okonkwo, ya shawarci Goodluck Jonathan da kada ya kuskura ya sake fitowa takara a zaben 2027, domin hakan ba zai yi masa daɗi ba.
A wani faifan bidiyo da shafin Symfoni ya wallafa a Youtube, Okonkwo ya ce Jonathan, ɗan asalin Jihar Bayelsa, ya riga ya yi wa ƙasa hidima a matsayin shugaban ƙasa na tsawon kusan shekara shida.

Source: Twitter
Okonkwo ya ce idan aka sake bai wa Jonathan damar mulki na shekaru huɗu, hakan na nufin ya yi shugabanci har tsawon kusan shekara goma, tun da ya riga ya yi kusan shida a baya.

Kara karanta wannan
'Mu fa sai Jonathan,' : Kungiyar Arewa ta dage tsohon shugaban kasa ya sake takara
“Shawarata ita ce kada Jonathan ya sake tunanin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027. Kada ma ya yi wannan tunanin."
"Mutanen nan da suka bata sunansa saboda kwadayin neman mulki a wancan lokaci, yanzu su ke da kasa, idan ya dawo za su batar da sunansa ne gaba daya," in ji shi.
3. Dr Abdul-Azeez Adediran (Jandor)
Jagoran Lagos4Lagos Movement, Dr. Abdul-Azeez Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa, Jonathan da kada ya saurari masu roƙonsa da ya sake tsayawa takara a 2027.
Adediran, dan takarar gwamnan Jihar Legas a ƙarƙashin inuwar PDP a 2023, ya ba Jonathan wannan shawara ne a wata hira da aka yi da shi, in ji rahoton Punch.
Ya ce, idan Jonathan ya sake tsayawa takara, zai jefa kansa cikin babban haɗari na siyasa, yana mai hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai kayar da shi cikin sauƙi.
Adediran ya ce mafi alheri ga Jonathan shi ne ya ci gaba zama a gefe, yana mai gargadin cewa “mutanen da ke tursasa masa tsayawa takara suna ruɗarsa ne kawai.”

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Source: Twitter
4. Sanata Adams Oshiomhole
Tsohon gwamnan Jihar Edo kuma sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya shawarci Jonathan da kada ya fada tarkon masu neman ya fito takara.
Sanata Oshiomhole ya gargadi tsohon shugaban kasar da ya hakura domin idan ya kuskura zai zubar da ragowar mutuncin da ya rage masa a siyasa.
Oshiomhole ya bayyana haka ne a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television, inda ya ce “abokan gaba ne kawai” za su so Jonathan ya sake tsayawa takara.
“Ina girmama shi ƙwarai. Amma ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun kayar da shi a da lokacin da PDP take kan ganiyarta.
"Mutumin da aka kayar a lokacin da PDP ke jan zarenta, to ina ganin abokan gabansa ne kadai za su tura shi ya sake shiga takara,” in ji Oshiomhole.

Source: Facebook
Sanatan ya ce bayan barinsa mulki, Jonathan ya zama mutum mai mutunci da daraja a idon jama’a, ya kamata ya rike wannan girma da ake ba shi maimakon dawowa siyasa.
5. Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike
Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi fatali da masu kiraye-kirayen Jonathan ya fito takara a zaben 2025.
Wike ya kara da cewa waɗanda ke kiran Jonathan ya tsaya takara su ne ’yan siyasan da suka yaudare shi a lokacin zaben 2015.
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce yanzu suna kokarin dawo da Jontahan ne domin tayar da rikici a Najeriya, ya shawarci tsohon shugaban kasar da kada ya biye masu.
Jaridar The Cable ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da 'yan jarida a birnin Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Satumban 2027.
Jonathan ya ba yan Najeriya shawara
A wani rahoton, kun ji cewa Goodluck Jonathan ya shawarci yan Najeriya su canza duk wani shugaba da ya gaza yin abin da ya dace.
Tsohon shugaban kasan ya ce idan dimokuraɗiyya ta kasa cika burin jama’a, hakan na iya buɗe kofa ga mulkin kama-karya.
Ya kara da cewa dole ne shugabanni su jajirce wajen aiwatar da irin dimokuraɗiyyar da za ta tabbatar da kyakkyawar makoma ga manyan gobe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



