"Ba Peter Obi Bane": Sanata Ya Fadi 'Dan Siyasa Mafi Muhimmanci a Yankin Igbo
- Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi magana kan tasirin Peter Obi a siyasar yankin Kudu maso Gabas
- Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa Peter Obi ba shi bane dan siyasa mafi muhimmanci a yankin ba
- Ya kuma tabo batun sakin jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kalu, wanda ke fuskantar shari'a kan ta'addanci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya kwatanta kansa da Peter Obi na jam'iyyar LP
Sanata Orji Uzor Kalu ya ayyana cewa shi ne ɗan siyasa mafi muhimmanci daga yankin Kudu maso Gabas, ba Peter Obi na jam’iyyar LP ba, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.

Source: Facebook
Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Sanata Kalu ya ce kan Peter Obi?
Tsohon gwamnan na jihar Abia ya raina tasirin Peter Obi a siyasar yankin Kudu maso Gabas.
Sanata Uzor Kalu ya ce nasarorin da ya cin mawa a siyasance, sun fi na Peter Obi nesa ba kusa ba.
"Ba shi ne shugabana ba. Ni ne ɗan siyasa mafi muhimmanci daga wannan yanki. Na taɓa lashe jihohi biyu karkashin jam’iyyar PPA. Na tsaya takarar shugaban kasa tun a 2007, inda na samu ƙuri’u miliyan 4.9."
"Mun cimma nasarori da yawa a lokacin PPA, muna da ministoci, jakadu, da sauran mukamai a lokacin Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.”
- Sanata Orji Uzor Kalu
Batun sake takarar shugaban kasa
Da yake amsa tambaya ko zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a nan gaba, Kalu ya ce shekaru ba za su hana shi yin takara ba, idan yana da lafiya da karfin jiki.
“Idan ina da lafiya kuma Allah Ya ba ni tsawon rai, zan iya sake tsayawa takara. Tambayar ba ta da alaƙa da shekaru, sai dai da cancanta."
- Sanata Orji Uzor Kalu
Me Kalu ya ce kan sakin Nnamdi Kanu?
A yayin tattaunawar, Kalu ya kuma tabo batun kiran a saki jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, inda ya gargaɗi mutane su guji yin magana a bainar jama’a kan shari’ar da har yanzu tana gaban kotu.

Source: Facebook
"Kun sani wannan lamari yana gaban kotu. Ba abu mai kyau bane na fara bayyana ra’ayina a fili ba tare da sanin matsayin kotu ko na shugaban kasa ba. Shugaban kasa na bibiyar yadda kotuna ke gudanar da aiki."
"Na tattauna wannan batu da shugaban kasa sau da dama, amma ba zan iya faɗa muku abin da muka tattauna ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kowa yana son a samu zaman lafiya."
- Sanata Orji Uzor Kalu
Peter Obi ya gana da Sheikh Pantami
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya gana da Sheikh Ali Isa Ibrahim Pantami.
Ganawar ta su ta zo ne bayan da Peter Obi ya ziyarci gidan tsohon ministan sadarwan da ke birnin tarayya Abuja.
Sheikh Pantami ya bayyana cewa sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasa yayin ganawar ta su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

