Gwamna Fintiri Ya Bayyana Abu na 2 da Ya Fi Kauna a Rayuwarsa bayan Addinin Musulunci
- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamwa ya ce jam'iyyar PDP na da matukar muhimmanci a wurinsa bayan addinin Musulunci
- Fintiri ya bayyana cewa kwamitin da yake jagoranta zai shirya gangamin PDP na kasa da za a yi a Ibadan cikin kwanciyar hankali
- Gwamnan ya kaddamar da kwamitin tsare-tsare a wani bangare na shirye-shiryen babban taron jam'iyyar PDP a garin Ibadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja- Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa ya ce bayan addininsa na musulunci, babu abin da ya dauka tamkar rayuwarsa kamar jam'iyyar PDP.
Gwamna Fintiri ya bayyana cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin an shirya gangamin taron PDP na kasa cikin kwanciyar hankali da nasara.

Source: Facebook
Fintiri, wanda shi shugaban kwamitin shirya babban taron PDP na kasa, ya fadi haka ne a taron kaddamar da karamin kwamitin tsare-tsare da ya gudana a Abuja, in ji Tribune Nigeria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya fara shirin taron PDP
Gwamna Fintiri ya jaddada cewa sababbin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) da za a zaba a gangamin PDP zai nuna wa yan Najeriya cewa jam'iyyar ta farfado.
Jam'iyyar PDP ta shirya gudanar da babban taronta mai taken ‘Ibadan 2025’ a garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.
Da yake jawabi a taron kaddamar da kwamitin wanda aka yi a Legacy House Abuja, Gwamna Ahmadu Fintiri ya ce:
“Bayan Musulunci, PDP ita ce abu na gaba da na sadaukar da kaina gare ta. Ina na tabbatar muku, bayan taron nan, sabon kwamitin NWC zai tabbatar da cewa PDP tana nan da rai, kuma ’yan Najeriya za su yi farin ciki.”
Fintiri ya kuma shawarci ’yan PDP da su yi watsi da waɗanda ya kira “’yan hayaniya” da ke ƙoƙarin kawo cikas, yana mai cewa a ƙarshe jam’iyyar za ta yi nasara bayan zaben shugabanni.

Kara karanta wannan
China ta zabi jiha 1 a Najeriya, za ta gina tashar wutar lantarki da wurin kasuwanci
Taron PDP: Yadda aka kafa kwamitin tsare-tsare
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Adamawa ya bayyana kwamitin tsare-tsare a matsayin “giwar taron”, inda ya ce an zaɓi mambobinsa a tsanaki saboda muhimmancin aikin da aka dora musu.
"Mun zaɓi fitattun mutane maza da mata, ciki har da Sanatoci, tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ’yan majalisar dokoki ta tarayya. Wannan ya nuna irin muhimmancin da PDP ta ba wannan kwamiti.
"Za mu tallafa muku domin ku yi nasara. Muna tabbatar muku da cewa a shirye muke mu yi duk mai yiwuwa don taron ya yi nasara," in ji shi.

Source: Twitter
Abin da Gwamna Mutfwang ya fada a taron PDP
A nasa jawabin, gwamnan Jihar Filato kuma shugaban ƙaramin kwamitin, Caleb Muftwang, ya yaba da jajircewar mambobin zuwa yanzu.
Gwamnan ya ce taron na Litinin wata dama ce ta haɗuwa da tattaunawa kafin a fara aikin tsara taron Ibadan gadan-gadan, in ji Daily Post.
Gwamna Fintiri ya yiwa fursunoni 6 afuwa

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Fintiri ya yi wa fursunoni shida afuwa a wani bangaren murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yancin kai.
Fursunonin da gwamnan ya yi wa afuwa ma daure a gidajen gyaran hali a jihar Adamawa bayan hukuncin da aka yanke masu kan laifuffukan da suka aikata.
Waɗanda gwamnan ya saki sun haɗa da: Wamari Godwin, Abraham Marksunil, David Paul, Ibrahim Adamu, Usman Inuwa, da Sani Yahaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
