Oshiomhole Ya Ba Jonathan Shawara kan Yin Takara da Tinubu a 2027
- Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ta tabo batun shawarar da ake ba Goodluck Jonathan kan yin takara a zaben 2027
- Adams Oshiomhole ya tunatar da Jonathan irin kimar da yake da ita a idon duniya wadda bai kamata ya bari ta zube ba idan ya dawo siyasa
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa mutanen da ba su son ganin ci gaban tsohon shugaban kasan ne kawai za su ba shi shawarar ya sake fitowa takara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, shawara kan zaben 2027.
Adams Oshiomhole ya shawarci Jonathan da kada ya amince da matsin lambar da wasu ke yi masa don shiga takarar shugabancin kasa a zaben 2027.

Source: Facebook
Adams Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin shirin 'Sunday Politics' na tashar Channels Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana rade-radin Goodluck Jonathan zai yi takara
Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda ya tsaya takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2015, ya sha kaye a hannun marigayi Muhammadu Buhari na APC.
A ‘yan watannin da suka gabata, an yi ta rade-radin cewa Jonathan na fuskantar matsin lamba daga wasu magoya bayansa da ke so ya sake tsayawa takara a 2027.
Sai dai, har yanzu bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan batun zai yi takara ko ba zai yi ba.
Me Oshiomhole ya ce kan takarar Jonathan?
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yin takarar Jonathan na iya lalata martabarsa da kimarsa a siyasance.
Hakazalika ya bayyana cewa makiyansa ne kawai za su so tsohon shugaban kasan ya sake tsayawa takara.

Kara karanta wannan
"Ka saurari matarka": Kusa a APC ya ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu a 2027
"Ina girmama shi sosai. Amma ta yaya Jonathan zai zama barazana gare mu? Mun doke shi a da lokacin da PDP ke da ainihin karfinta."
"Idan mutum yana a PDP a lokacin da take da tasiri kuma aka doke shi, to ni ina ganin makiyinsa ne kawai zai ba shi shawara ya sake yin takara."
- Adams Oshiomhole
Ya kara da cewa akwai wasu dalilai masu girma da za su kawo cikas ga Jonathan idan ya sake neman kujerar shugaban kasa.
“Na yi imani cewa ya nuna cewa mutum zai iya zama mai tasiri kuma a ci gaba da girmama shi har bayan ya bar mulki. Idan zan ba shi shawara, zan ce, 'ranka ya dade ka ci gaba da rike wannan matsayi naka'."
- Adams Oshiomhole
Sanatan ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya riga ya samu matsayi na mutunci da kima a idon duniya tun bayan barin mulki, don haka ya fi dacewa ya tsaya a hakan, maimakon neman dawowa cikin siyasa.

Source: Facebook
“Idan da ni ne shi, zan yi amfani da sauran rayuwata wajen kara gina wannan martaba da ya samu. Amma idan ya fito takara, za mu doke shi cikin sauki, saboda yanzu yankin Kudu ba ya tare da PDP, to daga ina zai fara?”

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027
- Adams Oshiomhole
Jandor ya shawarci Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa kusa a jam'iyyar APC, Abdul-Aziz Adeniran wanda aka fi sani da Jandor, ya ja kunnen Goodluck Jonathan kan yin takara a zaben 2027.
Jandor ya shawarci tsohon shugaban kasan cewa ka da ya bata lokacinsa wajen yin takara da Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi wa sauran 'yan siyasa fintinkau, domin babu wanda zai iya kayar da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
