Zaben 2027: Oshiomole Ya Yi Watsi da Barazanar El Rufa'i ga Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya yi martani ga ikirarin da takwaransa na Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi a kan Bola Tinubu
- Oshiomole ya fara da bayyana mamakin sauya shekar El-Rufa'i, wanda ya canja sheka zuwa ADC bayan ya samu sabani da APC
- Oshiomole, wanda ya yi ikirarin cewa El-Rufa'i abokinsa ne, ya ce nasarar Bola Tinubu ba ta da nasaba da Nasir El-Rufa'i
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata mai wakiltar yankin Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya yi magana a kan sauya shekar Nasir El-Rufa'i.
Oshiomole ya bayyana mamakinsa, inda ya bayyana cewa ba shi da masaniya a kan Malam Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP.

Source: Facebook
Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, a shirin Politics Today.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oshiomole ya yi 'mamakin' canja shekar El-Rufa'i
Jaridar Punch ta ruwaito Oshiomhole, ya bayyana cewa har yanzu tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yana cikin APC.
Ya kara da cewa:
“Eh, aboki na ne sosai.”
Sai dai da aka matsa masa cewa El-Rufai ya bar jam’iyyar ne tun a ranar 10 ga Maris, 2025, ya ce:
“Oh, ya fice? To, aboki na ne.”
Rahotanni sun tabbatar cewa El-Rufai, wanda daya ne daga cikin tushen kafa APC a 2013, ya fice daga jam’iyyar a hannun shugabannin mazabarsa a Kaduna, sannan ya koma SDP.
Ya bayyana cewa APC ta saba wa akidarsa, kuma jam’iyyar ta kauce daga kudurorin da suka kafa ta, saboda haka ya hakura da ita.
Oshiomole ya yi martani ga El-Rufa'i

Kara karanta wannan
Martanin da Sarki ya yi bayan zargin Peter Obi da rashin mutunta shi a sakon taya murna
Da aka tambayi Oshiomhole kan rahoton da ke cewa El-Rufai ya ce za a kora Tinubu zuwa Legas bayan zaben 2027, sai ya yi dariya.
Ya kuma ce El-Rufai ya taba yin hasashe kan Atiku da PDP, yana mai cewa:
“To, yanzu shi annabi ne? Mu yi tariya baya a kan abin da ya taba fada kan Atiku da PDP.”

Source: Facebook
Sai dai Oshiomhole ya tunatar da cewa duk da cewa APC ba ta ci Kaduna da Legas a zabe na baya ba, Tinubu ya ci zaben kasa baki daya, alamar cewa nasararsa ba ta dogara da El-Rufai ba.
Oshiomhole ya yabawa sabon gwamnan Kaduna kan kokarinsa na hade kan Arewa da Kudu na jihar, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen kwantar da tarzoma da nuna wariya ta addini da kabila.
El-Rufa'i: Ku yi hankali da Tinubu
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi tsauraran kalamai kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya zarge ta da mulkin kama-karya.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kai masa ziyarar goyon baya a Kaduna.

Kara karanta wannan
Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda
Atiku Abubakar ya ziyarci El-Rufai ne bayan wani hari da wasu 'yan daba da ake zargin jam’iyyar APC na da hannu suka kai masa yayin wani taron jam’iyyar ADC a jihar Kaduna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
