'Ba Jana'izar Mahaifiyar Shugaban APC Ta Kai Tinubu Jos ba,' Atiku Ya Yi Fallasa

'Ba Jana'izar Mahaifiyar Shugaban APC Ta Kai Tinubu Jos ba,' Atiku Ya Yi Fallasa

  • Dan takarar PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya ce ziyarar da Shugaba Bola Tinubu ya kai Jos ta nuna rashin tausayinsa ga ‘yan Najeriya
  • Mun ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya je Jos ne don jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda
  • Sai dai, Atiku ya ce ba jana'izar gyatumar Yilwatda Tinubu ya je ba, ya je ne yin shagali da 'yan jam'iyyarsa kamar yadda ya saba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ziyarar da ya kai Jos, babban birnin jihar Filato.

Legit Hausa ta rahoto cewa, a ranar Asabar, Tinubu ya ziyarci Jos domin halartar jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Atiku ya soki Tinubu kan ziyarar da ya kai Jos, inda ya ce ya fi damuwa da shagali fiye da halin da jama'a ke ciki
Hoton Shugaba Bola Tinubu da Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @officialABAT, @atiku
Source: Twitter

Atiku ya soki Tinubu kan zuwa Jos

Kara karanta wannan

Hankali ya kwanta: Babban alkawari da Tinubu ya yi ga Kiristocin Arewacin Najeriya

Sai dai, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Atiku ya ce Tinubu ya yi basaja da jana'izar mahaifiyar shugaban APC ya je Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya bayyana ziyarar a matsayin “jana’izar siyasa” da ta ba shugaban ƙasar damar yin shagali tare da manyan ‘yan jam’iyyar APC.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce:

“A yayin da sassan ƙasar nan ke fama da matsanancin rashin tsaro, da dubban mutane ke rasa rayukansu, abin takaici ne cewa Shugaba Bola Tinubu bai taɓa ganin ya dace ya kai ziyara a kowace daga cikin jihohin da ake kashe jama’a domin yin ta’aziyya ba.”

Ya ƙara da cewa Tinubu ya tuna da jihar Filato ne yanzu da ya je halartar taron 'yan jam'iyyarsa, ba wai don mutanen jihar sun dade suna fuskantar hare-hare ba.

“Ziyarar ta nuna rashin tausayin Tinubu” — Atiku

Atiku ya ci gaba da cewa halartar taron da Tinubu ya yi a Jos ya nuna yadda bai damu da mawuyacin halin da jama’a ke ciki ba.

“Abin takaici ne a ga cewa yayin da iyalai a Filato ke ci gaba da birne ‘yan uwansu, shugaban ƙasa ya zaɓi zuwa jana’izar siyasa maimakon ya jibinci jama’a a lokacin baƙin cikinsu."

Kara karanta wannan

Babu boye boye, an ji dalilin da ya sa Bola Tinubu bai jawo matarsa ta karbi musulunci ba

- Atiku Abubakar.

Ya ce abin da aka gani a tsakanin shugaban jam’iyyar APC da shugaban ƙasa shi ne: “Nuni da rashin tausayin jama’a da raina darajar rayuwar ɗan adam.”

Atiku ya tuna cewa daga Benue zuwa Neja da Kwara, yankin Arewa ta Tsakiya ya sha fama da mummunan tashin hankali a ‘yan shekarun nan, amma gwamnatin APC ba ta taɓa zuwa ta tausaya wa waɗanda abin ya shafa ba.

Atiku ya zargi Tinubu da son nishaɗi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma tuna cewa ko a lokacin da Tinubu ya kai ziyara jihar Benue a watan Yuni, bai je garin Yelewata — inda aka kashe mutane — ba, sai dai ya tsaya a Makurdi, inda suka yi nishadi.

“Yanzu kuma, ga shi ya je jihar Filato, ba don ya yi ta'aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa ba, sai don yin shagali da manyan jam’iyyarsa a lokacin da jama’a ke kuka,” in ji Atiku.

Kara karanta wannan

'Gadon Musulunci na yi': Tinubu ya fadi yadda yake rayuwa da matarsa Kirista

“Sakon a bayyane yake: wannan shugaban ƙasa ne da ya fi son biki fiye da tausayi — wanda ke samun farin ciki inda jama’a ke cikin azaba.
“Jama’ar Najeriya dai suna kallon abin da ke faruwa, kuma ba za su manta ba.”

- Atiku Abubakar.

Tinubu ya yi alkawari ga Kiristocin Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawari ga al'ummar Kiristocin Arewacin Najeriya yayin ziyarar da ya kai a jihar Plateau.

Shugaba Bola Tinubu ya ce burinsa shi ne haɗa kan al’ummar Najeriya, ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta yi adalci ga dukkan addinai.

Ya bayyana hakan ne a cocin COCIN da ke Jos yayin jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com