2027: Manyan Dalilan da Za Su Sanya 'Yan Arewa Su Iya Goyon Bayan Tinubu
- A yayin da ake shirye-shiryen zaɓen 2027, wasu masu ruwa da tsaki a Arewa na iya kara goyon bayan Shugaba Bola Tinubu saboda dalilai da dama
- Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da manyan ayyukan Arewa, ciki har da hanyoyin mota, layin dogo, gyara matatar mai da kuma saka jari a harkar noma
- Gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi sun yaba da kokarin gwamnatin Tinubu wajen tsaro da sauye-sauyen da ta kawo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Yayin da Najeriya ke kara matsawa kusa da zaɓen 2027, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar yabo da suka a lokaci guda kan manufofinsa.
Duk da kuncin tattalin arziki, wasu shugabannin Arewa na ganin Tinubu ya cancanci ci gaba da samun goyon bayansu.

Source: Twitter
Wasu 'yan Arewa na goyon bayan Tinubu
Tashar TVC News ta kawo rahoton cewa masu ruwa da tsaki a Arewa sun goyi bayan manufofin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin masu goyon bayan Tinubu har da gwamnoni, 'yan majalisu da sauran masu rike da mukamai.
Da dama daga cikinsu na ganin ya kamata yankin Arewa ya ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu a zaben 2027.
Ga wasu manyan dalilai guda biyar:
1. Ba 'yan Arewa mukamai a gwamnati
Da dama daga cikin ‘yan Arewa na jaddada cewa Tinubu ya tabbatar da cewa yankin ya samu ingantaccen wakilci a cikin gwamnatinsa.
'Yan Arewa na rike da manyan mukamai daga akataren gwamnatin tarayya zuwa ministocin tsaro, mai ba da shawara kan harkokin tsaro da babban hafsan hafsoshin tsaro.
Haka kuma, Tinubu ya kaddamar da hukumomin cigaban Arewa maso Yamma da na Arewa ta Tsakiya don karkatar da albarkatun tarayya zuwa yankin.
Sanata Ali Ndume ya yabawa Tinubu a matsayin shugaban da ke sauraron mutane lokacin da aka kara ba wasu 'yan Arewa 12 mukamai a watan Mayun 2025, rahoton TheCable ya tabbatar da labarin.
2. Manyan ayyukan ci gaba a Arewa
Masu goyon bayan Tinubu suna yin nuni da ayyuka da dama da ake daf da kammalawa a yankin Arewa.
Daga cikin ayyukan akwai hanyar mota ta Abuja–Kaduna–Kano, Layi dogo na Kano–Katsina–Maradi, gyaran matatar man Kaduna, aikin bututun iskar gas Abuja-Kaduna-Kano da kuma aikin hakar mai a filayen mai na Kolmani.
Bugu da kari, akwai ayyuka irin su babban titin Sokoto–Badagry da kuma fadada harkar noma, waɗanda aka tsara domin karfafa harkokin kasuwanci a Arewa.
Ana ganin wannan matakin saka jarin alama ce ta jajircewar gwamnatin tarayya ga cigaban yankin Arewa.
3. Shirye-shiryen noma da jin daɗin jama’a
Shugaba Tinubu ya kaddamar da wasu shirye-shirye da suka dace da magance kalubalen yankin Arewa.
Rahoton Premium Times ya nuna cewa an kirkiro sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobi don sabunta tsarin kiwon dabbobi, yayin da bashin ɗalibai da kuma shirye-shiryen koyar da sana’o’i ke karuwa a jihohin Arewa.
Jaridar The Punch ta ce gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yabawa Shugaba Tinubu kan kawo shirye-shiryen da suka amfani Arewa, musamman a bangaren noma da ilmi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan zargin jefa 'yan Najeriya miliyan 15 a bakin cikin talauci
Ya yabawa tsarin bada lamuni ga dalibai da shirin koyar da sana'o'i wanda ya bayyana a matsayin hanyoyin tsira ga miliyoyin matasa.
"Ba shugaban kasan da a tarihin Najeriya ya tallafawa gwamnatocin jihohi wajen bunkasa noma, kamar irin yadda Shugaba Tinubu yake yi yanzu."
- Gwamna Uba Sani

Source: Facebook
4. Kokari a fannin tsaro
Tsaro na daga cikin manyan matsalolin Arewa. Amma wasu gwamnonin sun yaba da ci gaban da aka samu a mulkin Tinubu.
Jaridar Tribune ta ambato gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, yana cewa an kashe fiye da shugabannin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 300 a mulkin Tinubu.
Hakazalika gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya jinjinawa shugaban kasa kan fifita tsaro da kuma samar da hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
5. Haɗa-kai da 'yan siyasan Arewa
Haɗin kan Tinubu da shugabannin Arewa da kungiyoyi na ci gaba da karfafa goyon bayan da yake samu a yankin
Jaridar The Nation ta ce a wani taron baje kolin ayyukan Tinubu a Kaduna, gwamnan jihar Gombe kuma shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya cika alkawuran da ya yi wa yankin a lokacin zaben 2023.
"Hadin gwiwa tsakanin Arewa da gwamnatin Tinubu ta samar da sakamako mai kyau, tun daga fannin samar da ababen more rayuwa, tsaro da mulki."
"Dole ne a 2027 mu maida biki inda a bisa hakan Shugaba Tinubu ya cancanci ya ci gaba da samun goyon bayanmu."
- Gwamna Inuwa Yahaya
Jam’iyyar APC ta goyi bayan Tinubu a hukumance don takarar zaben 2027, tana mai cewa yana da kyau ya ci gaba da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara.
Ga yawancin manyan ‘yan siyasa, haɗin kan Arewa da Kudu maso Yammacin Najeriya na ci gaba da kasancewa ginshikin daidaito, yayin da rarrabuwar kawunan 'yan adawa ke kara ƙarfafa damar Tinubu a zaben 2027.
Tinubu ya ba 'yan Najeriya shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da muhimmin sako ga 'yan Najeriya.
Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya kan su daina yin munanan kalamai ta fuska mara kyau ga kasar nan.
Ya nuna cewa Najeriya kasa ce ta mutane masu daraja wadda bai kamata ana zubar mata da kima a idon duniya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


