Tikitin 2027: Cacar Baki Ta Barke tsakanin Magoya bayan Obi da Atiku a ADC

Tikitin 2027: Cacar Baki Ta Barke tsakanin Magoya bayan Obi da Atiku a ADC

  • Magoya bayan Peter Obi sun tada bore a kan kalaman tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar kan tsaya wa takarar
  • A wani jawabi da Paul Ibe, hadimin tsohon 'dan takarar Shugaban Kasar ya fitar, ya ce babu inda Atiku ya janye tsaya wa takara a 2027
  • Kalaman sun tunzura magoya bayan Peter Obi, wanda ake kallon yana hararar tikitin takarar Shugaban Kasa a babban zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Magoya bayan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, sun maida martani kan kalaman Atiku Abubakar.

A ranar Alhamis ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ce ba zai janye wa kowanne dan takara ba a fafatawar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar ADC a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sahihancin zaben 2027 da tawagar tarayyar Turai

Magoya bayan Obi sun soki Atiku
Hoton Peter Obi da Atiku Abubakar Hoto; Mr. Peter Obi/Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar Obidient ta bayyana kalaman Atiku a matsayin wasa da hankalin jama'a gabanin zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obident ta yi martani ga Atiku Abubakar

Kungiyar magoya bayan Peter Obi ta jaddada cewa gwaninsu ba zai taba shiga siyasar sayen kuri’u ko sayen wakilai da Dala ba — wanda ya zama ruwan dare a siyasar Najeriya.

Shugaban kungiyar kuma tsohon mai magana da yawun yakin neman zaben Obi, Dr Yunusa Tanko, ya ce mai gidansa na da sabon tsarin siyasa da ya sha bamban da wanda ake yi a kasar nan.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar da cewa Obi ba zai shiga zaben fitar da gwani da za a rika sayan wakilai ba. Wannan shi ne abin da aka saba gani a sauran sansanonin siyasa. Yanzu kuwa, maimakon Naira, har da Dala ake siyan wakilai."

Ya kara da cewa wannan salon siyasa yana hana matasa masu kishi samun shiga harkar mulki, domin ba su da damar cin gajiyar sata ko kudin gwamnati.

Kara karanta wannan

Uwargidan Shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta samu sarauta a Gombe

Matsayar Atiku kan takara a 2027

A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce zai tsaya takara a zaben fitar da gwanin ADC, amma idan wani ya ci zaben, zai amince ya mara masa baya.

Atiku ya musanta shirin janye wa daga takara
Hoton Atiku Abubakar yana jawabi a wani taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya ce:

“Bayan nazarin bidiyon da rubutaccen hirar, babu inda Atiku ya ce ko ya nuna cewa yana shirin janye wa wani. Abin da ya fada shi ne: matasa da sauran ‘yan takara na da damar tsayawa takara, kuma zai goyi bayan wanda ya ci bisa gaskiya."

Atiku ya yi magana kan zaben 2027

A baya, kun samu labarin cewa tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya karɓi tawagar Tarayyar Turai (EU) a birnin tarayya Abuja, inda aka tattauna batutuwa da dama.

Daga cikin batutuwa masu muhimmanci da aka yi magana a kansu, akwai tabbatar da sahihancin zabukan Najeriya musamman na shekarar 2027 da ake jiran tsammani.

Tawagar EU ta kunshi Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, HE Gautier Mignot, da Barry Andrews, na majalisar Turai wanda ya jagoranci EU‑EOM a zabukan 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng