Siyasar Najeriya: Zuwa Kotu da Abubuwan da ake Fada kan Takarar Jonathan a 2027

Siyasar Najeriya: Zuwa Kotu da Abubuwan da ake Fada kan Takarar Jonathan a 2027

  • Ana ta fashin baki a kan ko tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na da damar sake tsayawa takara a 2027
  • Masu goyon bayansa na ganin doka ba ta hana shi ba, yayin da wasu ke cewa an riga an rantsar da shi sau biyu
  • A daya bangaren, masana shari’a sun ce batun zai iya kai wa ga kotu domin fassara abin da kundin mulki ya ce

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sabuwar muhawara ta barke a fagen siyasar Najeriya kan ko tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, na da damar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Magoya bayansa na cewa shi ne kadai jagoran da zai iya ceto Najeriya daga halin da take ciki, yayin da masu adawa ke jaddada cewa kundin tsarin mulki ya riga ya haramta masa.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka dawo manyan sarakuna

Shugaba Goodluck Jonathan a wani taro
Shugaba Goodluck Jonathan a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta hada wani rahoto na musamman kan ra'ayoyin masana a kan sahihancin takarar shugaba Jonathan a 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan: Martanin fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta tsoma baki cikin batun inda ta ce wadanda ke neman jawo Jonathan takara suna yin hakan ne don son zuciya.

Punch ta wallafa cewa Bayo Onanuga ya ce:

“Jonathan zai je kotu ya yi bayani. Lauyoyi za su tantance ko wanda aka rantsar sau biyu na da ikon sake tsayawa takara karo na uku.”

Sai dai tsohuwar mai ba Jonathan shawara, Josephine Washima ta bayyana cewa dawowarsa abu ne mai kyau domin a yanzu al’ummar kasar sun gane gaskiya kan gwamnatinsa.

Ta kuma nuna cewa kotun tarayya a Bayelsa ta riga ta fayyace cewa ba a hana Jonathan tsayawa takara ba.

Ra’ayin jam’iyya da wasu ’yan siyasa

Tsohon mataimakin shugaban PDP a Jihar Neja, Yahya Ability ya bayyana cewa Jonathan ne wanda ya fi karbuwa a Kudu.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Jonathan ya aika da muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Wasu shugabannin PDP daga Arewa, ciki har da Bala Mohammed da Sule Lamido, sun riga sun nuna goyon bayansu ga dawowar Jonathan.

A gefe guda, tsohon ministan yada labarai, Jerry Gana, ya bayyana cewa Jonathan zai tsaya takara kuma zai kayar da jam’iyyar APC a 2027.

Masana shari’a sun yi karin bayani

Barista Yusuf Mutumbi ya ce tsarin mulki ya fayyace cewa ba za a iya rantsar da mutum sau fiye da biyu ba.

Amma ya yi nuni da cewa a karon farko Jonathan ya gaji marigayi Umaru Musa Yar’Adua, ba rantsuwar cin zabe ya yi ba.

Ya kuma ce gyaran tsarin mulki na 2018 da ya haramta sake tsayawa idan aka rantsar da mutum sau biyu ba zai shafi Jonathan ba.

Sai dai Barista Abba Hikima ya ce akwai rarrabuwar kawuna kan fassarar wannan sashe, inda ya ce dokar za ta iya aiki a kan Jonathan.

Jonathan yayin da ya ziyarci David Mark
Jonathan yayin da ya ziyarci David Mark. ADC Vanguard
Source: Facebook

An ba Jonathan shawara kan 2027

Mai sharhi kan siyasa a Bayelsa, David West ya ce tsayawar Jonathan takara za ta iya sauya yanayin siyasar 2027 amma zai iya rage darajarsa idan bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

Ya bayyana cewa:

“Idan ya tsaya takara ya sha kaye, zai iya fuskantar matsin lamba da kuma durkushewar karfinsa a siyasa.”

Jonathan ya ziyarci David Mark

A wani rahoton, kun ji cewa a makon da ya gabata, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya kai ziyara gidan shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, a Abuja.

Sanata David Mark, wanda ya taɓa zama shugaban majalisar dattawa, ya yi aiki tare da Jonathan a lokacin mulkinsa daga 2010 zuwa 2015.

Duk da cewa kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ziyarar ba ta siyasa ba ce, masu sharhi na ganin tana da nasaba da shirye-shiryen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng