Atiku Ya Shirya Hakura da Takara da Tinubu a 2027? An Ji Gaskiyar Zance
- An yada wasu rahotanni masu nuna cewa Atiku Abubakar ya shirya hakura da takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasan ya fito ya fayyace gaskiya kan batun cewa ya shirya janyewa matashi takara a zaben da ake tunkara
- Atiku ya bayyana cewa sauya ma'anar abubuwan da ya fadi a cikin hirar da aka yi da shi cikin 'yan kwanakin nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan batun hakura da takara a zaben 2027.
Atiku Abubakar ya karyata ikirarin cewa zai janyewa matashi kafin zaɓen shugaban kasa na 2027.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko dai, Atiku ya riga ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Atiku ya bar jam’iyyar PDP wadda ya tsaya takarar shugaban kasa karkashinta a zaɓen shekarar 2023.
A watan Agusta kuma, Atiku da wasu manyan ‘yan adawa irinsu Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Peter Obi da sauransu, sun amince da yin amfani da jam’iyyar ADC domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Me Atiku ya ce kan fasa takara?
A cikin sanarwar, Paul Ibe ya bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin sauya hirar da ya yi da aka yi da Atiku kwanan nan.
Paul Ibe ya ce nazari mai zurfi kan bidiyo da fassarar hirar ya nuna cewa Atiku bai taɓa faɗa, nunawa, ko ma ya yi nuni da cewa yana da niyyar janyewa wani takara ba.
“Ya zama wajibi a fayyace gaskiya kan wasu rahotanni da suka taso daga hirar da Mai girma Atiku Abubakar ya yi da BBC Hausa, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka kawo."
“Bayan cikakken nazari kan bidiyo da rubutacciyar hirar, a cikin Hausa da kuma fassarar Turanci, a bayyane yake cewa babu inda tsohon mataimakin shugaban kasa ya faɗi, ko nunawa, ko ma ya yi alamun cewa yana shirin janyewa wani ba."
"Abin da Atiku Abubakar ya faɗa a fili kuma babu wani ruɗani shi ne cewa matasa, da kuma duk wani mai sha’awar tsayawa takara, suna da ‘yancin yin hakan."
"Ya kara jaddada cewa idan wani ɗan takara matashi ya yi nasara bayan zaben fitar da gwani na adalci, zai goyi bayan wannan ɗan takarar ba tare da wani jinkiri ba."
- Paul Ibe

Source: Facebook
Atiku ya caccaki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da yin rikon sakainar kashi da batun kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana cewa mutane da dama sun koma masu bara duk da dumbin albarkatun da Najeriya take da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

