2027: Tsofaffin Tsagerun Neja Delta Sun Bayyana Matsayarsu kan Tazarcen Tinubu

2027: Tsofaffin Tsagerun Neja Delta Sun Bayyana Matsayarsu kan Tazarcen Tinubu

  • Ana ci gaba da maganganu kan batun tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027
  • Kungiyar tsofaffin tsagerun Neja Delta sun shiga sahun masu nuna matsayarsu kan sake zaben Tinubu
  • Ta bayyana irin ci gaban da yankin Neja Delta ya samu a karkashin shekaru biyu na mulkin Mai girma Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Delta - Kungiyar tsofaffin tsagerun Neja-Delta (NDEAF) ta yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Kungiyar ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga tazarcen Shugaba Tinubu a 2027.

Tsagerun Neja Delta sun goyi bayan tazarcen Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jawabi. Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa tsofaffin ‘yan tawayen sun yi wannan alkawarin ne a yayin gangamin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

An yi gangami kan nasarorin Bola Tinubu

Gangamin wanda aka gudanar a birnin Warri na jihar Delta, ya kuma hada da murnar manyan nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu wajen farfaɗo da kasar nan a fannoni daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci

Wanda shirya ya gangamin, “Janar” Emma Satu, a yayin jawabinsa ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta a kasar, shekaru biyu da suka gabata a karkashin gwamnatin Shugaba Tinubu sun kasance masu muhimmanci ga Najeriya.

Emma Satu ya tabbatar da cewa yankin Neja-Delta ya samu kulawa sosai ta fuskar samar da ababen more rayuwa, gina hanyoyi, samun mukamai a matakin tarayya da sauran muhimman abubuwa da dama.

Shugaba Tinubu ya samu goyon baya

Emma Satu ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta dauki manyan matakai ta hanyar kawo manufofin da suka shafi tattalin arziki, ilimi, lafiya, ababen more rayuwa, wutar lantarki da sauran muhimman fannoni.

"Goyon bayanmu ga shugaban kasa ya samo asali ne daga kauna, kulawa da kuma jin daɗin haɗin kan da yankin Neja-Delta ke samu a gwamnatinsa."
"Neja-Delta ba ta taɓa samun irin wannan ba, domin muna jin daɗin zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a duk faɗin yankinmu."
"Shi ya sa muka taru a nan a wannan rana ta musamman ta bikin ranar ‘yancin Najeriya domin sake bayyana cikakken goyon bayanmu ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027."

Kara karanta wannan

"Mun ceto Naira," Tinubu ya tabo batun darajar kudin Najeriya a jawabin ranar 'yanci

"Duk da cewa akwai ƙalubale da muke fuskanta a kasar nan, shekaru biyu da suka gabata a karkashin Shugaba Tinubu sun kasance masu muhimmanci ga Najeriya."
"Yankin Neja-Delta ya samu kulawa ta musamman ta fuskar samun ababen more rayuwa, gina hanyoyi, mukamai a gwamnatin tarayya da kuma sauran abubuwa masu muhimmanci."

- Emma Satu

Shugaba Tinubu ya samu goyon baya
Shugaban kasa Bola Tinubu a wajen kaddamar da cibiyar al'adu ta Wole Soyinka. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya ja hankalin 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nuna muhimmancin girmama kasar nan ga 'yan Najeriya.

Mai girma Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su daina kalamai cikin mummunan salo kan kasar, inda ya nuna cewa ko kadan hakan bai dace ba.

Shugaban kasan ya bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su yi imani da kasar, tare da yin aiki don ganin cewa ta samu ci gaban da ake bukata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng