Kwankwaso Ya Yi Rashi, Jigon Tafiyar Kwankwasiyya Ya Koma APC a Kano
- Tafiyar Kwankwasiyya ta samu nakasu a jihar Kano bayan ficewar wani jigo da ya ba ta gudunmawa matuka tsawon shekaru
- An tabbatar da cewa jagoran Kwankwasiyya a Gobirawa da ke Dala, Alhaji Amadu Danfulani ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC
- Danfulani ya zargi jam’iyyar NNPP da manufofin da ke cutar da jama’a, ya kuma bayyana farin cikinsa na hada kai da shugabannin APC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano – Daya daga cikin jagororin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ya watsar da tafiyar inda ya koma jam'iyyar APC.
Dan siyasar daga unguwar Gobirawa da ke karamar hukumar Dala, Alhaji Amadu Danfulani ya tabbatar da ficewarsa daga tafiyar.

Source: Facebook
Kano: Jigon tafiyar Kwankwasiyya ya bar Kwankwaso
The Nation ta ce Danfulani ya sanar da sauya shekar daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a jiya Talata 30 ga watan Satumbar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Danfulani ya bayyana rashin jin dadinsa kan manufofi da shirye-shiryen jam'iyyar NNPP a jihar Kano, inda ya ce ba su dace da bukatun talakawa ba.
Ya kara da cewa shi da dubban magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar domin neman mafaka a jam'iyyar APC mai mulki.
Taron tuba da sauya shekar ya gudana a sakatariyar APC ta jihar Kano da ke kan hanyar Hotoro-Maiduguri, cewar Daily Post.
A wurin ne shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas, wanda aka wakilta da Shehu Aliyu Ungoggo, ya karbi sabon dan jam’iyyar tare da sauran wadanda suka sauya sheka.

Source: Facebook
Jiga-jigan APC ta suka halarci bikin a Kano
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar da suka hada da babban daraktan raya kogunan Hadejia Jama’are (HJRBDA), Rabiu Suleiman Bichi,
Sannan akwai shugaban matasan APC na Kano da Arewa maso Yamma, Labaran Kura, da sauran shugabannin jam’iyyar a Dala da Gobirawa.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ko da Rabiu Musa Kwankwaso kansa na da damar dawowa jam’iyyar muddin ya bi ka’idodi da dokokin jam’iyyar.
APC ta kara da cewa sauya shekar Danfulani da dubban mambobin NNPP wata babbar nasara ce a shirye-shiryen su kafin zaben 2027.
Alkawarin Danfulani ga Bola Tinubu, 'yan APC
Danfulani ya bayyana farin cikinsa kan komawarsa APC, inda ya yi alkawarin hada kai da shugabannin jam’iyyar domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon jigon tafiyar Kwankwasiyya ya kuma yi alkawari ga dukkan ’yan takarar jam'iyyar APC a babban zaben 2027 domin taimaka musu yin nasara a zabukan da ke tafe.
Barau Jibrin ya karbi daruruwan 'yan Kwankwasiyya
A wani labarin, daruruwan mambobin NNPP da Kwankwasiyya daga Bagwai da Shanono sun fice daga jam’iyyar tare da komawa APC a Abuja.
Masu sauya shekar sun jefar da jajayen huluna da suka kasance alamar Kwankwasiyya domin nuna katse alaka da tsohuwar jam’iyyarsu.
Sanata Barau Jibrin ya yi alkawarin cewa APC za ta ci gaba da kare muradun al’umma tare da kara ayyuka masu amfani ga jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

