Taron Tsintsiya: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Kallon da Tinubu ke Yi wa 'Yan Hadaka
- Hadiman shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya yi magana a kan kokarin da 'yan hadaka ke yi ya kara dunkule wa gabanin zaben 2027
- Ya bayyana hadakar da cewa taron 'yan siyasa ne da lokacinsu ya riga ya wuce, kuma ba su da sauran tasiri ko katabus a siyasar Najeriya
- Ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu bai damu ba, kuma babu wata hadakar adawa da ke yi masa barazana yayin da ya ke yi wa jama'a aiki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya yi watsi da ƙoƙarin da wasu jiga-jigan 'yan adawa ke yi na kafa kawancen siyasa.
Ya bayyana su a matsayin mutanen da ta su ta ƙare a siyasar Najeriya, masu kishin kansu da kuma fusatattu sabodda mulki ya kwace masu.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa AbdulAziziz ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a cibiyar NUJ da ke Kano a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
AbdulAziz AbdulAziziz: 'Yan adawa ba sa tsorata Tinubu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Abdulaziz ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai damu ba ko kaɗan da irin wannan ƙoƙari na kawancen 'yan adawa.
A kalamasa:
"Zan iya tabbatar muku cewa shugaban ƙasa ba ya cikin wani hali na damuwa. Wadanda ke kokarin kafa wadannan kawance, yawancinsu sun riga sun ƙare a siyasa. Mutane ne da ba su da nauyi ko tasiri a siyasa da za su iya tayar da jijiyoyin wuya ga gwamnati ko ma shugaban ƙasa."
Ya ƙara da cewa wasu daga cikinsu sun rika tsayawa takara sau da dama amma ba su kai labari ba, aboda haka yanzu duk ransu a bace ya ke.
AbdulAziz ya ce:
"Kuma gaskiyar magana, tauraron su na ƙara dusashewa ne, ba ya haskakawa,."
Tinubu ya yi aiki a Najeriya - AbdulAziziz AbdulAziziz
Abdulaziz ya jaddada cewa shugaba Tinubu yana tafiyar da mulkinsa bisa tsari na gyara ƙasa, ba siyasa ba, kuma ana iya ganin abubuwan da ya ke yi.
Ya bayyana misalai irin su shirin lamunin dalibai, gyaran tallafin mai, da manyan ayyukan abubuwan more rayuwa da ake yi a ƙasar.

Source: Facebook
Ya ce gwamnati na ci gaba da manyan ayyuka a Arewa, kamar layin bututun gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano, titin Abuja-Kaduna-Kano, da layin dogo na Kano-Katsina-Maradi.
Shugaba Tinubu ya yi maraba da takarar Jonathan
A baya, kun samu labarin cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa tana maraba da shirin tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, na sake neman takara a zaben 2027.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, ya ce suna maraba da Jonathan da sauran ‘yan takara da ke son fafata wa da APC a babban zaben.
Onanuga ya ƙara da cewa, duk da maraba, bai manta da gazawar da Jonathan ya yi a lokacin mulkinsa ba, don haka ‘yan Najeriya ba za su yarda a koma matsalolin baya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


