Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Maraba da Takarar Tsohon Shugaba Jonathan a 2027
- Fadar Shugaban Kasa ta yi maraba da shirin tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan na sake neman takara a zaben 2027
- Tsohon Ministan Yada Labarai, Farfesa Jerry Gana ya yi ikirarin cewa Jonathan zai dawo ya karbe mulkin Najeriya a zabe mai zuwa
- Kalaman Farfesa Gana na zuwa ne bayan shafe tsawon lokaci ana rade-radin cewa akwai yiwuwar Jonathan ya dawo siyasa gadan-gadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa tana maraba da dawowar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, kuma har zai nemi takara a zaben 2027.
Idan ba ku manta ba an dade ana hasashe da jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar na shirin dawowa harkokin siyasa gadan-gadan tare da neman takara a zabe na gaba.

Source: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa a ranar Lahadi, tsohon Ministan Yada labarai, Farfesa Jerry Gana, ya ce Jonathan zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a inuwar PDP.
Jerry Gana ya ce Jonathan zai nemi takara
Yayin da yake magana da ’yan jarida jim kaɗan bayan taron PDP a Minna, Jihar Neja, a ƙarshen mako, Farfesa Jerry Gana ya ce:
“A 2015, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya ce jinin 'yan Najeriya ya fi burinsa muhummanci. Bayan ya sauka, wani shugaba ya yi shekara takwas, ga wani yanzu ya yi shekara biyu."
"Yanzu yan Najeriya sun ga banbanci, komai ya fito fili, sun dawo auna rokonmu mu dawo da abokinmu, tsohon ahugaban kasa, Goodluck Jonathan
"Zan iya tabbatar muku cewa Jonathan zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a inuwar PDP, kuma ya kamata mu shirya mu zaɓe shi domin ya dawo kan mulki.”
Fadar Shugaban Kasa ta yi maraba da Jonathan
A martanin da ya yi cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce sun marabawa da dawowar Shugaba Jonathan.

Kara karanta wannan
"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027
Sai dai Onanuga ya yi ikirarin cewa 'yan Najeriya ba su manta ba, za tuna da gazawar da ya yi a lokacin mulkinsa, in ji Leadership.
“Mu na maraba da Shugaba Jonathan da sauran ’yan takara a zaɓen 2027. Su ne suka ruguza tattalin arziki a da, amma mun san ’yan Najeriya ba su manta da duk abin da ya faru ba, kuma ba za su bari a koma baya ba.
“’Yan siyasa irin su Jerry Gana suna son jawo shi ya shiga takara ne don su cimma burikan zuciyarsu na siyasa, addini da ƙabilanci.
"Amma za su watse su bar shi shi kadai a tsakiyar hanya, kamar yadda suka yi masa a 2015, su bar Jonathan, mutum mai sauƙin hali cikin rudani.”
- Bayo Onanuga.

Source: Facebook
Jonathan ya gana da shugaban ADC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya kai ziyara ga shugaban jam'iyyar hadakaADC, Sanata David Mark.
Wannan ziyara ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin cewa Jonathan na iya shiga takarar shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi babban rashi, tsohon shugaban hukumar PSC ya riga mu gidan gaskiya
Duk da ba a bayyana ainihin manufar tattaunawar ba, masana harkokin siyasa na ganin cewa ziyarar ta ƙara jefa haske kan yiwuwar Jonathan ya nemi takara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
