Shirin APC Ya Fara Rushewa, Babban Jigo da Magoya Bayansa Sun Fice daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Yobe ta samu koma baya yayin da daya daga cikin manyan jiga-jiganta ya fice daga cikinta
- Hon. Mohammed Bello, tsohon dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa ya mika takardar ficewarsa daga APC ga shugabannin jam'iyyar
- Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyun adawa na ADC da PDP sun fara zawarcin dan siyasar tare da magoya bayansa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Babban jigon APC, wanda dan siyasa ne sananne a jihar Yobe, Hon. Mohammed Bello, ya fice daga jam’iyya mai mulki.
Hon. Mohemmed Bello ya bayyana matakin da ya dauka na raba gari da APC a matsayin “fita daga kangin da yake ciki.”

Source: Getty Images
Jigo da magoya bayansa sun bar APC
Bello, wanda tsohon ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa (Zone A) ne a ƙarƙashin inuwar APC, ya sanar da ficewarsa tare da dimbin magoya bayansa, cewar rahoton Vanguard.
Dan siyasar ya tabbatar da hakan a wata wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar APC na mazabar Gwange, a birnin Damaturu.
A takardar, wacce ta shiga hannun manema labarai, Hon. Mohammed ya ce matakin da ya dauka ya fara aiki ne nan take.
Meya sa Hon. Mohammed Bello ya bar APC?
A wani bangaren wasikar, fitaccen dan siyasar ya ce:
“Na rubuto muku wannan wasiƙa ne don sanar da ku a hukumance game da shawarar da na yanke ta ficewa daga jam’iyyar APC daga yau.
"Ban yanke wannan shawara haka kurum ba, sai da na yi dogon tunani kan dabi’ata, akiduna da kuma inda jam’iyyar ta dosa.
"Bayan dogon nazari, na yanke cewa abin da yafi dacewa da ni da al’ummata shi ne na fice daga jam’iyyar APC a wannan lokaci.”
Hon. Mohammed Bello ya bayyana godiyarsa bisa damar da ya samu ta yin takara a tsawon lokacin da ya shafe a matsayin dan jam'iyyar APC.
Ya ce mu'amala da gogewar da ya samu za su kasance masu amfani gare shi har abada.

Source: Facebook
ADC da PDP sun fara zawarcin dan siyasar
Bugu da kari, ya hada da katinsa na APC ya aika wa shugabannin jam'iyyar domin tabbatar da matakin da ya dauka.
A halin da ake ciki, majiyoyi sun bayyana cewa shigabannin jam'iyyar hadaka watau ADC sun fara zawarcin Mohammed Bello da magoya bayansa.
Ita ma, babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta fara ƙoƙarin jawo shi ya shiga cikinta a yayin da ake ci gaba da shirin babban zaɓen 2027, in ji rahoton Daily Post.
Gwamna Mbah na shirin komawa APC
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Peter Mbah na Jihar Enugu ya gama shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki.
Majiyoyi masu karfi da ke kusa da gwamnan sun bayyana cewa Peter Mbah ya amince zai koma APC ne bayan tattaunawa da wasu manyan jiga-jigai.
Wadanda suka taimaka wajen jawo gwamnan har ya amince da shiga APC sun hada da tsofaffin gwamnoni, Chimaroke Nnamani da Sullivan Chime.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

