Zaben 2027: Rikici Ya Kunno Kai tsakanin Magoya bayan Peter Obi da Jam’iyyar ADC

Zaben 2027: Rikici Ya Kunno Kai tsakanin Magoya bayan Peter Obi da Jam’iyyar ADC

  • Rashin jituwa na shirin kunno kai a tsakanin magoya bayan tsohon 'dan takarar Shugaban Kasa, Peter Obi da hadakar ADC
  • A karshen mako ne Shugaban Kungiyar Obidients, Dr. Yunusa Tanko ya zargi ADC da saba alkawarin da aka daukar wa Obi
  • Amma jam'iyyar hadakar adawa ta yi gaggawar martani, inda ta kare kanta tare da bayyana matsayar Tanko da cewa ta kashin kai ce

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa ba ta yanke matsaya dangane da yadda za ta raba tikitin takarar shugaban kasa ba a zaben 2027 mai zuwa.

Kakakin yada labarai na kasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi a kan batun.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

ADC ta yi martani ga masoya Peter Obi
Hoton Mai Magana da Yawun ADC, Bolaji Abdullahi Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya kuma karyata zargin da shugaban kungiyar Obidient, Dr. Yunusa Tanko, na cewa an ADC ta karya alkawari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ADC ta kare kanta

A cewar Abdullahi, babu yadda za a zargi jam'iyyar ADC da karya alkawari bayan ba ta dauki irin wannan alkawari ba ko makamancinsa.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ba ta taba daukar irin wannan alkawari ga kowanne bangare na hadakar siyasa da ake kokarin kafawa ba.

'Yan ADC sun yi martani ga Obidients
Tsohon 'dan takarar Shugaban LP, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

A cewar Bolaji Abdullahi, har yanzu, babu wata tattaunawa da aka yi kan tsarin yankin da 'dan takarar Shugaban Kasa zai fito.

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar Obidients ta bakin Dr. Tanko ta soki yadda ADC ta ki bayyana matsaya a kan rabon mukaman siyasa, musamman ma na shugaban kasa.

ADC ta caccaki magoya bayan Obi

Bolaji Abdullahi, wanda kuma tsohon ministan wasanni ne, ya bayyana kalaman Dr. Yunusa Tanko a matsayin abin da zai iya jawo rarrabuwar kai da rikita al’umma.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Jonathan ya hadu da shugaban hadaka na Jam'iyyar ADC

Ya kara da cewa babu Dr. Tanko a cikin wadanda ke da hurumi ko matsayin magana da sunan jam’iyyar ko hadakar siyasar ba.

Bolaji Abdullahi ya kara da cewa babu tabbacin Tanko ya tuntubi Peter Obi kafin ya fitar da irin wannan matsaya.

Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce ADC na da damar yin sassauci da wasu abubuwa bisa ga bukata, amma hakan ba yana nufin za a yarda da irin kalaman tunzuri ba.

Ya jaddada cewa:

“Shugabannin ADC ba su tattauna batun tsarin yankin ba. Ta ya za mu karya alkawari da ba mu taba yi ba? Ra’ayin Tanko ba ya wakiltar matsayin Peter Obi.”

Obidient ta tanka jam'iyyar ADC

A baya, mun wallafa cewa kungiyar Obidient, wacce ke mara wa tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi baya, ta mayar da martani kan sabon umarnin da jam’iyyar ADC.

Jam'iyyar hadakar ta bayar da sabon umarni, ta bukaci ‘yan hadaka da su yi murabus daga tsofaffin jam’iyyunsu domin mayar da hankali kacokan kan ADC yayin da ake tunkarar 2027.

Kara karanta wannan

ADC ko ADA: 'Yan hadaka sun kammala zabar jam'iyyar da za su yi takara a 2027

A cikin sanarwar da Shugaban Kungiyar, Yunusa Tanko ya fitar, ya ce suna bayar da gudunmawa mai yawa ga hadakar jam'iyyun siyasa, saboda haka sun yi mamakin umarnin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng