An Yi Auren Dan Tsohon Minista, Atiku, El Rufai da Manya Sun Cika Cocin Abuja

An Yi Auren Dan Tsohon Minista, Atiku, El Rufai da Manya Sun Cika Cocin Abuja

  • An daura auren dan tsohon ministan Sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi a cikin wani coci da ke Abuja inda manyan yan siyasa suka halarta
  • Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tare da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai sun samu damar halartar bikin
  • Har ila yau, Gwamna Alex Otti na Abia da ministoci da kuma sanatoci ciki har da Sanata Simon Lalong da sauran manya na daga cikin mahalarta taron

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, Gwamnan Abia, Alex Otti, da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun hadu a Abuja.

Atiku, El-Rufai da sauran manyan yan siyasa a Najeriya sun halarci bikin ɗan Rotimi Amaechi da aka yi a Abuja.

El-Rufai da Atikusun halarci aurem da Amaechi
Hotunan bikin dan Rotimi Amaechi cikin coci a Abuja. Hoto: Rt Hon. Chibuike R Amaechi.
Source: Facebook

Atiku, El-Rufai sun shiga coci a Abuja

Kara karanta wannan

Magana ta kare, tsohon gwamna ya zama Sarki mai martaba a Najeriya

Legit Hausa ta samo bayanai game da bikin daga shafin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda ya wallafa a Facebook har da bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, matar tsohon shugaban ƙasa, Patience Jonathan, matar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Dolapo Osinbajo sun halarci bikin.

Sauran sun hada da tsohon gwamnan Filato, Solomon Lalong da wasu fitattun baki sun samu halarta.

Jan hankali daga babban Fasto ga ma'auratan

A wajen bikin, Fasto Steve Dedua ya ja hankalin sababbin ma’aurata Chikamkpa da Anita da su kasance masu hakuri, su jingina da Allah a aurensu.

Ya ce Chikamkpa da Anita suna gaban Ubangiji a matsayin shaida ga amincinsa, don haka Allah zai ci gaba da ɗaukaka zaman aurensu.

Ya ce:

“Ina cewa daga farko Allah ya halicci namiji da mace, ya haɗa su domin su zama ɗaya, don haka babu wanda zai raba su."
Atiku da El-Rufai sun halarci auren dan Amaechi a Abuja
Haduwar Atiku da Nasir El-Rufai yayin taron siyasa a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Shawarwarin da aka ba ma'auratan a Abuja

Faston ya nuna damuwarsa kan rahoton da ya bayyana kasashen da ke da yawan sakin aure, inda Najeriya ta zo a matsayi na 11 a duniya.

Kara karanta wannan

Nadin Sarauta: Sarkin Musulmi ya isa Ibadan, ana dakon Tinubu da Atiku

Rev. Dedua ya ƙara da cewa:

“Anita da Chikamkpa sun fito a yau suna sanar da duniya cewa ba za su shiga wannan jerin ba.”

A wajen liyafar aure, Gwamna Alex Otti ya ba sababbin ma’aurata shawara kan sulhu, ya ce su koyi tattaunawa idan rikici ya taso tsakaninsu.

Dr. Chikamkpa Amaechi da Anita sun yi aure na gargajiya a makon da ya gabata a Abuja kafin bikin coci na jiya Asabar, cewar rahoton Tribune.

Ganin El-Rufai a coci ya jawo magana

Kun ji cewa an yi ta yada wasu hotuna sun nuna Malam Nasir El-Rufai a coci, inda aka ce yana kokarin jawo limamai don zaben 2027 da shirin kifar da Bola Tinubu.

El-Rufai ya halarci jana’izar tsohon kwamishinan Anambra, Mathias Anohu ne, ba wai ya je neman goyon bayan Fastoci ba kamar yadda aka yada a baya.

An tabbatar da cewa hoton daga jana’iza ne da aka gudanar a Okija, kuma El-Rufai ya wallafa hakan da kansa a kafar sadarwa wand aya saba da jita-jitar da ake yadawa a baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com