Yadda Kwankwaso zai Yi Alaka da Ganduje idan Ya Koma APC da Wasu Abubuwa 2

Yadda Kwankwaso zai Yi Alaka da Ganduje idan Ya Koma APC da Wasu Abubuwa 2

  • Ana hasashen siyasar Kano za ta canza sosai idan Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da komawa jam’iyyar APC mai mulki
  • Hakan na iya tayar da sabuwar dambarwa tsakaninsa da tsohon abokinsa kuma abokin hamayyarsa a yau, Abdullahi Umar Ganduje
  • Ana hasashen jam’iyyar NNPP da ke mulkin Kano na iya shiga cikin rikice-rikice masu tsanani har ma ta rasa tasiri gaba ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Siyasar jihar Kano na ci gaba da zama jigon tattaunawa a Najeriya sakamakon rade-radin yiwuwar komawar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kwankwaso, wanda aka shaida da samun dimbin mabiya a Kano, ya jagoranci nasarar NNPP a babban zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da sauran wakilai.

Kara karanta wannan

NiMet: Ruwa da tsawa za su shafi harkokin jama'a a Kano, wasu jihohin Arewa

Kwankwaso tare da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje
Kwankwaso da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje. Hoto: All Progressive Congress|Saifullahi Hassan
Source: Twitter

BBC Hausa ta hada wani rahoto kan abubuwa da ake hasashen za su iya faruwa a siyasar Kano idan har ya Kwankwaso ya koma APC.

An yi hasashen ne bayan maganganunsa na baya-bayan nan sun sake tunzura hasashe cewa ya na iya yin sulhu da APC kafin 2027, lamarin da ka iya juyar da taswirar siyasa a jihar.

Alaka tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Daya daga cikin manyan abubuwan da ake duba shi ne yadda dangantakar Kwankwaso da Abdullahi Ganduje za ta kasance idan suka hadu a jam’iyya daya.

A baya, sun yi aiki tare tsawon shekaru a matsayin gwamna da mataimaki, kafin rikici ya raba su bayan 2015 lokacin da Ganduje ya karɓi mulki.

Tun daga lokacin, adawar su ta yi tsami, inda kowanne ya shiga jam’iyyar daban. Masana sun yi nuni da cewa idan Kwankwaso ya dawo APC, sabuwar dambarwa za ta tashi tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Makomar 'yan adawa a jihar Kano

NNPP ta karɓi ragamar gwamnati a Kano a 2023 bayan ta doke APC. Wannan ya bai wa jam’iyyar ƙarfin zama babbar 'yar adawa a matakin ƙasa.

Sai dai idan Kwankwaso ya bar ta, tambaya ita ce wace jam’iyya za ta ci gaba da rike tafiyar adawa a Kano?

Wasu masu sharhi kan siyasa na ganin ADC na iya zama madadin, muddin ta samu jagora mai ƙarfi a jihar.

Haka kuma ana ganin PDP da ta taɓa zama babbar 'yar adawa za ta iya farfadowa idan manyan ‘yan siyasa suka dawo cikinta, musamman idan shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takara.

Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf
Kwankwaso tare da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Makomar jam’iyyar NNPP a jihar Kano

An yi hasashen cewa idan Kwankwaso ya fita daga NNPP tare da mabiyansa, jam’iyyar ka iya rushewa gaba ɗaya ko ta koma ƙarama mai tasiri a kananan matakai.

Legit ta rahoto cewa yanzu ma akwai rikici a cikinta, inda aka samu ɓangarori biyu: na Kwankwaso da kuma na waɗanda ke cewa su ne ‘yan asali.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki: Sabon rahoto ya cire Kano daga ta 1 a sakamakon NECO

Masana sun ce saboda Kano ce jihar da NNPP ke da karfi sosai a Najeriya, ficewar Kwankwaso zai iya haifar da ƙarancin wakilci a majalisu da kuma rasa karfin ikon siyasa.

APC ta yi watsi da Rabiu Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Kano ta yi watsi da maganar sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kakakin jam'iyyar APC na jihar ne ya bayyana cewa ba su yarda da sharadin da Rabiu Kwankwaso zai kafa musu ba.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da rade radin cewa Rabiu Kwankwaso zai koma APC kafin zaben shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng