Da Gaske Kwankwaso Ya Rubuta Wasikar Shiga APC? Madugun NNPP Ya Yi Bayani

Da Gaske Kwankwaso Ya Rubuta Wasikar Shiga APC? Madugun NNPP Ya Yi Bayani

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba shi da hannu a labarin da ake yadawa cewa ya rubuta wasiƙar komawa APC
  • Hakan na zuwa ne bayan an ce tsohon gwamnan Kano ya tura wasiƙa ga shugabancin APC na ƙasa a Abuja
  • Tun a kwanakin baya ake cigaba da yada jita jitar cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta jita-jitar da ke cewa zai koma APC.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cewa ya rubuta wata wasika ga shugaban APC na kasa a shirin sauya sheka.

Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro karin bayanin da Rabiu Kwankwaso ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: APC ta yi watsi da sharadin Kwankwaso na sauya sheka

Kwankwaso ya rubutawa APC wasika?

Kwankwaso ya bayyana cewa bai rubuta wasiƙar komawa kowace jam’iyya ba, yayin da ya yi kira ga al’umma su dogara sahihan hanyoyin yada bayanai daga ofishinsa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙara rade-radin cewa akwai tattaunawa tsakanin Kwankwaso da jagorancin APC na ƙasa kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar.

A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, Kwankwaso ya bayyana cewa rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta ba su da tushe.

Sanarwar ta kara da cewa duk wani labari da ke fitowa ba tare da izini daga ofishinsa ba bai kamata a ɗauke shi a matsayin gaskiya ba.

Dalilin yin martanin Kwankwaso

Tun da farko dai wasu 'yan APC ne suka ce Kwankwaso ya shiga tattaunawa da shugabancin jam’iyyar a Abuja, lamarin da ya haifar da rade-radi kan yiwuwar dawowarsa.

Daily Trust ta wallafa cewa jigon APC da ya yada jita jitar ya kara da cewa APC za ta rungumi duk shawarar da shugabanninta suka ɗauka a matsayin mafi alheri ga jam’iyya.

Kara karanta wannan

Ana batun canja sheka, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da shugaban APC, Nentawe

Kwankwaso: Jitar jitar 'yan APC a Kano

Majiyoyi daga Kano APC a Kano ma sun ce sun tabbatar da cewa akwai rahoton cewa Kwankwaso ya tura wasu sharudda na dawowa jam'iyyar da ya bari a baya.

Kafin Kwankwaso ya karyata labarin, wani daga cikin shugabannin jam’iyyar ya ce:

“Mun san da wasiƙar amma ba lokacin tattaunawa ba ne yanzu. Idan ya na son dawowa, ba mu da matsala da shi, muna maraba da shi.”

APC ta yi watsi da dawowar Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa kakakin jam'iyyar APC a jihar Kano, Ahmed Aruwa ya bayyana cewa ba su bukatar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a tafiyar siyasar su.

Aruwa ya ce jam'iyyar APC ta sha samun nasara a baya ba tare da taimakon Kwankwaso ba, saboda haka ba su bukatar sharudan dawowar shi tafiyarsu.

Ya kara da cewa ba Kwankwaso ba ne ya kafa jam'iyyar APC a Kano, domin a cewarsa, Malam Ibrahim Shekarau ne ya taka muhimmiyar rawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng