Atiku Abubakar Ya Fusata, Ya Yi Magana kan Alkawarin Fifita Yarbawa idan an Zabe Shi
- Tsohon 'dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya musanta cewa yana da wata alaƙa da wani mai suna Kola Johnson har da kiran kansa mashawarcinsa
- Ya bayyana cewa wasu mayaudara marasa alkibla ne ke ƙirƙirar labaran ƙarya domin ɓata masa suna a idon jama'a da sunan mashawartansa kan yada labarai
- Atiku ya ce ba zai lamunci ƙage ko yaɗa bayanan ƙarya da ke da nufin kawo rabuwar kai tsakanin ƙabilu ba bayan an ce ya yi alƙawarin fifita Yarbawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan wata sanarwar da aka danganta da shi.
Ya fara jawabinsa da karyata dangantaka da wani da ake kira Kola Johnson, wanda aka bayyana a cikin wata sanarwa a matsayin mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa Sanarwar da mai ba Atiku shawara kan harkokin labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Alhamis ta ce babu wani lokaci da Atiku ya taɓa ɗaukar Kola Johnson aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya barrranta kansa da wani labari
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya ce duk wani bayani da ake dangantawa da sunan Kola Johnson game da Atiku ƙarya ne.
Sanarwar da Paul Ibe ya fitar ta ce:
“Atiku Abubakar bai taɓa ɗaukar Kola Johnson a matsayin mai ba shi shawara, mataimaki ko abokin aiki ba. Sanarwar da aka danganta da sunansa karya ce kuma ya kamata a yi watsi da ita."
A cewar sanarwar, abin da ya fi tada hankali shi ne ƙaryar da ke cewa gwamnatin Atiku za ta fifita wata kabila guda daya kacal.
Atiku ya nuna yatsa ga gwamnati
Atiku ya bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na kirkirar labaran bogi domin haifar da tashin hankali da ƙara raba kawunan al’umma.

Kara karanta wannan
Atiku zai fifita Fulani idan ya samu mulki? Wazirin Adamawa ya kare kansa ga Yarbawa

Source: Facebook
Sanarwar ta ce:
“Bincikenmu ya nuna cewa fadar shugaban ƙasa ce ke ɗaukar nauyin waɗannan mutane domin su ƙirƙiri labaran ƙarya da nufin ɓata sunan shugabannin hamayya."
Sanarwar ta kuma bukaci dukkannin kafafen yada labarai da suka wallafa wannan labarin su janye shi nan da nan, tare da tabbatar da labari ya fito daga ofishin yada labaransa kafin a buga.
Atiku ya kuma bayyana cewa 'yan kabilar Yarbawa suna da muhimmanci a rayuwarsa, kasancewar yana da dangantaka ta aure da su tun shekarun 1970s.
Ya ce:
“Na auri matata ta farko, Titi, Bayerabiya ce, kuma muna da ‘ya’ya huɗu tare. Har yanzu muna tare, kuma ina girmama dangantaka ta da yankin Yarbawa."
Ya ƙara da cewa Yarbawa na da wayewa da ilimi, kuma yana ganin su a matsayin dangi da abokan aminci, ba bisa siyasa kawai ba.
Kawuna sun rabu kan Atiku da Tinubu
A baya, mun wallafa cewa rikici ya barke a tsakanin magoya bayan tsohuwar jam’iyyar CPC, da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa a kan wanda za a zaba a shekarar 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa an samu sabani a kan shawarar wanda za a mara masa baya a zaɓen 2027 — ko Atiku Abubakar na hadakar adawa ko Bola Tinubu na jam'iyya mai mulki.
Sabanin ya biyo bayan ziyarar da wasu tsofaffin jiga-jigan CPC su ka kai gidan Atiku a Abuja, inda suka bayyana cewa za su mara masa baya a zaben 2027 da ke tunkaro wa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

