Ganduje Ya Fito da Bayanai kan Maganar Sauya Shekar Kwankwaso zuwa APC
- Tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi magana bayan taro da shugabannin jam’iyya a don ƙarfafa haɗin kai
- Ganduje ya ce ba ya ganin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai dawo APC mai mulkin kasa saboda wasu kalamansa na baya
- Ganduje ya kuma tabo zancen sauke shi daga shugabancin jam'iyyar APC da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano — A ranar Alhamis, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci wani taro na jam’iyyar.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibril, shugabanni da jagororin jam'iyyar APC sun hallara taron.

Source: Twitter
BBC Hausa ta rahoto cewa Ganduje ya ce an tattara su ne domin ƙara hada kawunan 'yan jam’iyyar da kuma shimfiɗa shirin shawo kan rikice-rikicen siyasa a nan gaba.
APC: Maganar Ganduje kan Kwankwaso
A cikin jawabin sa, Ganduje ya ce ya ji rade-radin cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, na iya komawa APC, amma ya ce bai ɗauki wannan batu da muhimmanci ba.
Ganduje ya ce ya nuna shakku kan sauya shekar Kwankwaso ne saboda halin da aka riga aka saba da shi a siyasa.
Duk da haka Ganduje ya kara da cewa duk wanda ya ga dacewa zai iya shigowa jam’iyyar kuma za a yi maraba da shi amma bisa sharadi.
Sai dai ya bayyana cewa ko da Kwankwaso ya dawo APC za su kira su da 'yan APC masu amai su lashe saboda maganganu marasa dadi da ya yi a kan jam'iyyar a baya.
Tsohon gwamnan ya ce a matsayinsu na jam'iyya, APC tana maraba da kowa.
Ganduje kan Kwankwaso da Shekarau
Da aka tambaye shi ko za a haɗa Kwankwaso da wasu kamar Shekarau, Ganduje ya bayyana cewa ra’ayi ne mai kyau idan ana son haɗin kai.
Ya ce shugabannin APC suna da gogewa wajen gudanar da gwamnati kuma za su iya bayar da shawarwari masu amfani idan aka haɗa su.

Source: Facebook
Maganar sauka daga shugabancin APC
Tsohon gwamnan ya ce sauke shi da aka yi a shugabancin APC ba wani abu ba ne kuma shugaban kasa bai yi masa laifi ba da aka sauya shi.
Abdullahi Ganduje ya ce tsarin APC ya ginu a kan raba mukamai ne bisa yankunan Najeriya, kuma 'yan wani yanki sun ga cewa su ne suka cancanci rike shugabancin APC a yanzu.
Ya bayyana cewa a kan haka ne aka sauke shi aka mika ragamar shugabancin jam'iyyar ga Arewa ta Tsakiyan Najeriya.
A wani sako da shi ma Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook, ya ce za su cigaba da hada kai domin samar da nasarar APC a jihar Kano da Najeriya.
Ganduje ya musuluntar da maguzawa
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya jagoranci musuluntar da maguzawa sama da 200.
Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka yi a gidan shi da ke jihar Kano a makon da ya wuce.
Ya bayyana cewa dama ya saba daukar nauyin karatun Al-Kur'ani, musuluntar da maguzawa da addu'o'i ga Kano da kasa baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


