Barau Ya Hango Abin da Mutanen Kano Za Su Yi Wa Tinubu a 2027
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Sanata Barau ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya nuna kauna ga mutanen Kano da Arewacin Najeriya baki daya
- Ya bayyana cewa za a rama biki ga shugaban kasan a lokacin babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna kauna ga jihar Kano.
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa za a saka wa shugaban na Najeriya da goyon baya mai karfi a babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce Sanata Barau Jibrin ya yi wannan bayanin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar daga jihar Kano da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 25 ga watan Satumban 2025.
'Yan jam'iyyar APC a Kano sun yi taro
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje, karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Atta, Sanata Kawu Sumaila.
Sauran sun hada da Abubakar Bichi, shugaban kwamitin majalisar wakilai kan kasafin kuɗi, Abubakar Bichi, tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Gaya, Sulaiman Bichi, da kuma wasu ‘yan majalisa da dama na yanzu da na baya.
Me Sanata Barau ya ce kan Tinubu?
“Muna tare da shi kwarai domin ya nuna mana ƙauna. Ya samar mana da manyan makarantun gaba da sakandire, ayyukan raya kasa, da sauran shirye-shirye."
"Mun roki jama’armu su ci gaba da goyon bayan shugaban kasa da jam’iyyar APC tare da yin addu’a ga kasarmu.”
- Sanata Barau Jibrin
Sanata Barau ya bayyana cewa taron ya yi nazari kan matsayin jam’iyyar APC a Kano da ma Najeriya, inda aka cin ma matsaya cewa jam’iyyar mai mulki tana kara ƙarfi da tasiri.
"Mun amince baki ɗaya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jiharmu da Najeriya baki daya aiki."
"Mun kirga ayyuka da dama da ake aiwatarwa a Kano da sauran yankunan Arewacin kasa."
"An kuma naɗa mutane da dama daga jihar Kano da Arewa gaba ɗaya mukamai a gwamnatin tarayya."
- Sanata Barau Jibrin

Source: Twitter
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa bunkasar jam’iyyar APC a Kano ba ta rasa nasaba da matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka domin rage radadin talauci da wahalhalu ga jama’a.
A nasa jawabin, Dr Abdullahi Ganduje ya ce jam’iyyar APC a Kano tana nan da karfinta, duk da cewa ta sha kaye a zaɓen gwamnan jihar na 2023.
Tinubu ya aika sako ga Majalisar Dinkin Duniya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika sako ga Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaba Tinubu ya shawarxu majalisar dattawa da ta yi gaggawar rungumar sauye-sauye don ta tsira da tasirinta.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa bambanci tsakanin maganganun Majalisar Dinkin Duniya da ayyukanta yana barazana ga yadda jama'a ke aminta da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

