Gwamnan Jigawa Ya Bayyana Matsayarsa kan Tazarcen Tinubu a 2027

Gwamnan Jigawa Ya Bayyana Matsayarsa kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Ana ci gaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan tazarcen shugaban kaaa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027 duk da bai ce zai yi takara ba
  • Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba kan salon mulkin da Shugaba Tinubu yake yi a Najeriya
  • Ya nuna cewa za su yi bakin kokari domin ganin cewa shugaban kasan ya sake komawa kan madafun iko a karo na biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kwararo yabo ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Namadi ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin ta kwarai, wanda hakan ya sanya ’yan Najeriya alfahari da ita ba tare da la’akari da siyasa ko bambancin kabila ba.

Gwamna Namadi ya goyi bayan tazarcen Tinubu
Hoton gwamnan Jigawa, Umar Namadi da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @uanamadi, @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wajen kaddamar da kungiyar 4+4 Tinubu/Danmodi Mobilisation Campaign Group a Manpower Development Institute (MDI), a birnin Dutse.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa Gabdi ya ce gwamnoni ne matsalar kasar nan, ya ba talakawa shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Namadi ya ce kan Tinubu?

Gwamna Namadi ya ce manufar Renewed Hope ta samar da kyakkyawan yanayi na ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa da bunkasa jama'a a Jigawa da Najeriya baki daya.

Umar Namadi ya samu wakilci daga wajen mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Hon. Lawan Garba,

Gwamnan ya yi kira ga kungiyar da ta wayar da kan al’umma kan manyan ayyuka da shirye-shiryen da gwamnatin APC ta aiwatar, rahoton jaridar PM News ya tabbatar da labarin.

"Wanda ya yi aiki mai kyau a wa’adin farko, ya cancanci ya sake samun wani. Jigawa tana tare da Shugaba Bola Tinubu, kuma za mu tabbatar da nasararsa a 2027, Insha Allah."

- Gwamna Umar Namadi

Gwamnan ya kara da cewa jama’ar Jigawa sun gamsu da irin jagorancin da Shugaba Tinubu ke yi, wanda ya inganta rayuwar al’umma ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya shawarci Atiku Peter Obi kan takara da Tinubu a 2027

Gwamna Namadi ya yabi Shugaba Tinubu
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @uanamadi
Source: Twitter

An nada shugaban kungiyar kamfen

A yayin taron, an nada shugaban karamar hukumar Garki, Hon. Adamu Hudu Kore, a matsayin shugaban kungiyar wayar da kan jama’a a jihar Jigawa.

A jawabin amsarsa, Adamu Hudu Kore ya tabbatarwa jama’a cewa kungiyar za ta gudanar da kamfen na wayar da kan jama’a domin ci gaba bayyana nasarorin da Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi suka cimma.

Ya kuma yi alkawarin gudanar da ayyukan kungiyar bisa doka da tsarin zabe na Najeriya, tare da bin ka’idojin jam’iyyar APC.

Hakazalika ya ce ayyukan kungiyar za su kasance masu karfafa zaman lafiya, ci gaba da fadada imokuraɗiyya gabanin babban zaben 2027.

Gwamna Namadi ya bada hutu a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bada hutun kwana guda

Gwamna Namadi ya bada hutun ne a ranar Laraba, 27 ga watan Agustan 2027 domin bikin murnar cika shekara 34 da kafa jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027

A cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan Jigawa ya fitar, gwamnatin ta ce hutun ya shafi ma’aikata da mazauna jihar domin su huta da yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa zaman lafiya da ni’imomin da ya ba jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng